23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

HURIWA ta nemi a sauke kwamishinan ‘yan sandan Kano akan rashin binciken tashin bam a jihar

LabaraiHURIWA ta nemi a sauke kwamishinan 'yan sandan Kano akan rashin binciken tashin bam a jihar

Kungiyar kare hakkin bil’adama, wacce ke rubutu akan kare hakkin bil’adama ta Najeriya (HURIWA), a ranar Alhamis ta bukaci a sauke kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Sama’ila Dikko, a kan “saurin yanke hukunci” cewa gobarar da ta tashi a yankin Sabon Gari na jihar a ranar Talata gobarar gas ce ba tashin bom ba, Vanguard ce ta ruwaito.

Huriwa, a wata takarda da shugaban kungiyar na kasa, Emmanuel Onwubiko ya fitar, ta zargi shugaban ‘yan sandan da hanzarin sanar da abun da ya haddasa annobar ba tare da wani bincike ba, duk da yadda “mazauna yankin da ganau suka tabbatar a tattaunar talabijin cewa wutar ta tashi ne sanadiyyar tashin bom.

Wutar taci titin Aba na yankin sabon gari a safiyar Talata, wacce akayi tunanin ta lashe rayukan mutane tara bayan raunata tarin jama’a.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar (Dikko) yayin jawabi a kan aukuwar lamarin ya ce, gobarar gas ce ta tashi daga shagon masu walda kusa da wata makarantar kasa da sakandiri da ta firamere.

Sai dai, ganau sun musanta maganar shugaban ‘yan sandan inda sukace “ba gobarar gas ne ya haddasa lamarin ba, sai dai fashewar bom, soboda tsananin jijjiga.

A cewar Onwubiko,
“Ganau sun zanta da Arise TV, kuma sun musanta maganar ‘yan sandan.
Shedun sun bada labarin yadda wani ‘dan kunar bikin wake ya tada bom, wanda ya lashe rayuwarsa da ta mutane da dama, amma ‘yan sanda sukayi karya.

“HURIWA tayi kira ga korar kwamishinan ‘yan sandan bisa saurin yanke hukunci game da musabbabin tashin wutar kafin ya yi wani bincike.

“Haka zalika, muna kira ga gwamnatin jihar Kano da na tarayya da kungiyar gwamnonin kudu da su tallafa wa wadanda lamarin ya auku da su saboda wadanda aka sa bom din dominsu Inyamurai da sauran ‘yan kudu ne da suka cika Sabon Garin Kano.

“Har ila yau, muna kira ga bincikar lamarin don gano asalin mukasudin tashin wutar, duba da a halin yanzu ganau na alakanta hakan da tashin bom.”

Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishina a jihar Kano

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya nada Alaramma Ahmed Sulaiman a matsayin kwamishina a jihar sa, BBC ta ruwaito.


Ya nada shi ne a matsayin kwamishinan ilimi na biyu kamar yadda Alaramman ya tabbatar da mukamin a shafinsa na Facebook.

A wallafar da ya yi, ya nuna godiyarsa kwarai ga gwamnan inda ya sa hotunan da su ka dauka tare.


Cikin mutanen da su ka samu halartar taton nadin nasa gar da shugaban kungiyar izala na kasa, Sheikh Abdullahi Balalau da kuma Sheikh Kabir Haruna Gombe, sakataren kungiyar na kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe