29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Kano: Masu garkuwa da mutane sun sako basaraken da su ka ɗauke, sun yi ram da mai kai kuɗin fansa

LabaraiKano: Masu garkuwa da mutane sun sako basaraken da su ka ɗauke, sun yi ram da mai kai kuɗin fansa

Abdulyahyah Ilo, magajin garin Karfi cikin ƙaramar hukumar Takai, a jihar Kano, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane.

Sai dai masu garkuwa da mutanen, sun riƙe wani farfesa a jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kano (KSTU), Wudil, Huzaifa Karfi, wanda yaje kai kuɗin fansar.

Masu garkuwa da mutanen sun halaka mutane a ƙauyen

Daily Trust ta rahoto cewa masu garkuwa da mutanen sun halaka mutane shida, waɗanda su kayi ƙoƙarin ceto basaraken lokacin da su kaje ɗaukar sa.

Sun dai farmaki ƙauyen ne akan babura guda 3 daga jihar Bauchi ta cikin dajin Ringim a jihar Jigawa.

An tabbatar da sako basaraken

Wani mazaunin yankin, Musa Sa’ad, ya tabbatar da sakin basaraken daga hannun waɗanda su kayi garkuwa da shi.

Ya bayyana cewa mafarauta da ‘yan sakai sun cafke ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen a cikin daji waɗanda ke da hannu a satar mutane da kashe-kashen da akayi a ƙauyen Ƙarfi.

Sun ƙarbi kuɗin fansar sannan su ka riƙe Dr Huzaifa bisa kama mutumin su da ‘yan sakai su ka yi. Sun buƙaci da a sako musu mutumin na su kafin su sako shi.

Wani ɗan’uwan basaraken, Yusuf Ismail, ya tabbatar da an sakin na shi inda yanzu haka ake duba lafiyar sa a asibiti.

Da aka tuntuɓi, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, bai da masaniya dangane da lamarin amma yayi alƙawarin zai biyo baya da ƙarin bayani.

‘Yan bindiga sun sako Lakcarar da su ka yi garkuwa da ita, sun riƙe ‘yar ta tare da su

A wani labari na daban kuma, ‘yan bindiga sun sako lakcara da su kaƴi garkuwa da ita, sai dai sun riƙe ɗiyar ta a hamnun su.

Ramatu Abarshi, wata lakcara dake koyarwa a makarantar Polytechnic ta Kaduna, wacce ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da ita tare da diyar ta da kuma direban ta, sati uku da suka gabata, ta sami shaƙar iskar yanci.

An yi garkuwa da sune akan titin Kachia-Kaduna, yayin da suke dawowa daga aikin jin kai.

Abdallah Isma’il Abdallah
babban jami’in gudanarwa na gidauniyar
Barkindo Rahama Initiative, wacce Dr Abarshi ta kafa, shine ya tabbatar da sakin malamar, kamar yadda ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe