28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

‘Yan bindiga sun sako Lakcarar da su ka yi garkuwa da ita, sun riƙe ‘yar ta tare da su

Labarai'Yan bindiga sun sako Lakcarar da su ka yi garkuwa da ita, sun riƙe 'yar ta tare da su

Ramatu Abarshi, wata lakcara dake koyarwa a makarantar Polytechnic ta Kaduna, wacce ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da ita tare da diyar ta da kuma direban ta, sati uku da suka gabata, ta sami shaƙar iskar yanci.

An yi garkuwa da sune akan titin Kachia-Kaduna, yayin da suke dawowa daga aikin jin kai.

An tabbatar da sakin na ta

Abdallah Isma’il Abdallah
babban jami’in gudanarwa na gidauniyar
Barkindo Rahama Initiative, wacce Dr Abarshi ta kafa, shine ya tabbatar da sakin malamar, kamar yadda ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust.

Yace, bayan an sake ta a ranar Alhamis, an garzaya da ita wani asibiti da ba’a bayyana ba, domin a binciki lafiyar ta.

Abdallah ya bayyana cewa, an sake ta ne bayan tattaunawa wa da masu garkuwar da ita, amma bai bayyana ko an basu kudin fansa ba, kafin sakin nata.

Amma diyar ta Ameerah tare da direban ta suna rike a gurin masu garkuwar.

Yayi ƙarin bayani

An dai ɗauke ta ne akan hanyar dawowa daga rabon kayan tallafi

Idan za’a iya tunawa, a ranar 24 ga watan Afirilun 2022, yan bindiga suka tsare tsohuwar shugabar sashen koyon kimiyyar lantarki da kayan lantarki wato (Electrical and electronics engineering ) ta makarantar Kaduna Polytechnic, tare da ‘yar ta a lokacin da suke dawowa daga rabon kayan masarufi ga marasa karfi, a yankin Mariri, dake ƙaramar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun ɗauke basarake a jihar Kaduna, sun buƙaci man fetur da katin waya a matsayin kuɗin fansa

A wani labari na daban kuma, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Kaduna, sun faɗi abubuwan da su ke buƙata a matsayin kuɗin fansa.

‘Yan bindiga sun ɗauke Mr Ayuba Dodo Dakolo, magajin garin Rijana, cikin ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jaridar Daily Trust ta samo cewa an ɗauke magajin garin ne tare da wasu manoma a ƙauyen Kurmi kusa da Chikwale a cikin ƙaramar hukumar ta Kachia.

Garin Rijana dai yana akan hanyar Abuja-Kaduna kuma yayi ƙaurin suna wajen kai hare-hare inda ‘yan bindiga su ke tare hanya suna ɗauke matafiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe