24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

An yanke wa wani rago hukuncin shekara 3 a gidan kaso bisa halaka wata tsohuwa

LabaraiAn yanke wa wani rago hukuncin shekara 3 a gidan kaso bisa halaka wata tsohuwa

An yanke wa wani rago hukuncin shekara 3 a gidan kaso bayan ya halaka wata mata a sanadiyyar tunkuyin ta.

Shafin LIB ya rahoto cewa ragon ya hari matar mai suna Adhieu Chaping, mai shekaru 45, inda ya tunkure ta sau da dama a ƙirji kafin ta rasu a ƙarshen mako.

An bayyana yadda hukuncin zai kasance

Daga cikin hukuncin, ragon zai kwashi wani lokaci a tsare a wani sansanin sojoji bayan shugabannin gargajiya sun masa hukunci a ƙasar Sudan ta kudu.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan’uwan matar an sanar musu da cewa mai ragon zai basu shanu 5 a matsayin diyya.

Ragon ya kai mata hari ta hanyar tunkurin ta a haƙarƙari inda nan take tsohuwar ta mutu.

Jam’in ɗan sanda Elijah Mabor ya shaidawa gidan rediyon Sudan’s Eye

Wannan shine abinda ya faru a Rumbek East a wani wuri da ake kira  Akuel Yol.

Aikin mu a matsayin ‘yan sanda samar da tsaro da kuma rabon faɗa. An kamo ragon inda yanzu haka hannun mu a ofishin ‘yan sanda na Maleng Agok Payam

Zaa bayar da diyyar kisan da ragon yayi

Hukumomi sun tabbatar da cewa iyalan biyu sun amince cewa mai ragon zai bayar da shanu 5 biss yarjejeniƴar da aka cimmawa da shugabannin ƙauyen.

An bayyana sunan mutumin da yake da ragon a matsayin Duony Manyang Dhal.

Za a bayar da ragon kyauta ga iyalan Chaping da zarar an sako shi daga gidan kaso, bisa tanadin doka.

Sai da iyalan biyu su ka sanya hannu akan yarjejeniyar domin tabbatar da ita inda shugabannin garjajiya su ka zama shaidu.

Kotu ta yanke wa Bature hukuncin kisa bayan ya halaka matarsa ‘yar Najeriya da diyarsa

A wani labari na daban kuma, kotu ta yankewa wani bature hukuncin kisa bisa halaka matar sa da ɗiyar sa.

Gwamnatin jihar Legas ta zargi Mista Nielsen da kashe matarsa ​​da ‘yarsa da misalin karfe 3.45 na safe a gidansu da ke tsibirin Banana.

Wata babbar kotu a Legas a ranar Juma’a ta yanke wa wani ɗan katsar Denmark, Peter Nielsen, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe matarsa ​​da ‘yarsa ‘yar Najeriya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe