28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

2023: Maza sun gaza; cikin watanni 6 zan dawo da Najeriya kan turba, ‘yar takarar shugaban ƙasa

Labarai2023: Maza sun gaza; cikin watanni 6 zan dawo da Najeriya kan turba, 'yar takarar shugaban ƙasa

‘Yar takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Uju Ken Ohanenye, ta nuna damuwar ta kan abinda ta kira da gazawar maza wajen samar da shugabanci mai kyau a Najeriya. Jaridar Vanguard ta rahoto

Za ta kawo ƙwarewa a gwamnatin ta

A yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tv a Legas, ranar Laraba, ‘yar takarar tayi nuni da cewa za ta kawo ƙwarewa da ɗaɓi’ar uwa wajen mulki domin kawo sauyi.

Nayi shiru tsawon wannan lokacin. Ba na son na shiga cikin lamuran, amma duba da yadda abubuwa ke tafiya ba zan iya cigaba da yin shiru ba, saboda na damu ganin yadda abubuwa ba su tafiyya yadda ya dace. Na lura cewa mutanen Najeriya na buƙatar jawabai.

Na yanke shawarar yin takara. Ina son kawo cigaba. Ina so na kawo sauyi, maza sun gaza. Saboda haka na shiga takara domin ‘yan Najeriya na buƙatar uwa. Sun rasa uwa. Maza ne kawai ke tafiyar da lamura.

Ohanenye ta ce, idan aka zaɓe ta matsayin shugabar ƙasa, za ta mayar da hankali wajen samar wa da matasa aiyukan yi domin magance matsalolin rayuwa na yau  da kullum.

Ta ƙara da cewa gwamnatin ta, za ta samar da ingantaccen muhalli ga matasa domin yin nasara.

Ta bayyana hanyoyin da za ta bi wurin samar da aiyukan yi

Dangane da hanya ƙwaƙƙwara wajen samar da aikin yi, ta bayyana cewa za ta rage dogaron da Najeriya ke yi kan man fetur, sannan ta mayar da hankali wurin haɓɓaka noma domin samar da arziƙi.

Ohanenye, ta roƙi mata da kada halin shugabancin ƙasar nan yake a halin yanzu ya sa guiwoyin su yin sanyi, inda take cewa dole ne mata su yi la’akari da goben ‘ya’yan su su fito a dama da su a harkokin siyasa.

Zaɓen 2023: Shugaba Buhari na da ɗan takarar da yake son ya gaje shi, inji Femi Adesina

A wani labari na daban kuma, Hadimin shugaba Buhari, Femi Adesina ya bayyana cewa shugaba Buhari na da ɗan takarar da ya ke son ya gaji kujerar sa.

Femi Adesina, mai bawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce shugaba Buhari na da wanda ya ke son ya gaje shi a 2023, amma ba zai ambaci sunan mutumin ba. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Hadimin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV’s Politics a jiya Alhamis, 12 ga watan Mayun 2022

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe