23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ke ‘yar maye, sana’armu kwalelenki: Martanin Jaruman Kannywood ga Safara’u

LabaraiKannywoodKe 'yar maye, sana'armu kwalelenki: Martanin Jaruman Kannywood ga Safara’u

Bayan tsohuwar jarumar Kannywood, Safiya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u Kwana Casa’in, ta saki wakoki tana yi wa jaruman masana’antar habaici, an samu masu mayar mata da martani.

Kamar yadda wakarta ta Kwalelenka ta bayyana, ta kira jaruman masana’antar da ‘yan wahala inda ta ce ta bar sana’ar.

Duk da dai da farko babu wanda ya kula ta, daga bisani jarumai sun fito suna nuna mata cewa sana’ar ce ta barta, ba ita ce ta bar sana’ar ba.

Wata jaruma wacce ta kira kanta da Mero ta saki bidiyon waka wacce ta yi shige da ta Safara’un, inda ta kirata da ‘yar maye.

Ta ce sana’ar fim sana’a ce mai tsafta don haka ba za su sanya marasa daraja irinta a cikin harkar ba.

Cikin wakar har habaici ta yi dange da bidiyon da ya dinga yawo akan Safara’u na tsiraici, har ta ce ita dai ba za ta iya tura wa saurayi ba.

Har ila yau, jaruma Umma Shehu ma ta mayar mata da martani inda ta ce ai fim ne ya kaita duk inda za ta je kuma saboda fim ne aka santa.

Ta kalubalanceta inda ta ce ta dena amfani da sunan Safara’u in har da gaske ta ke ta tsani fim.

Ta ci gaba da cewa:

“Wallahi da ni ce ke, duk wanda ya kira ni da Safara’u sai mun yi shari’a da shi. Kin je kin yi bidalarki, an kore ki daga fim kin dawo kuma kina kame-kame.

“Ai fim shi ne gatanki. Saboda fim ne har ki ka yi suna aka san ki.”

Ai ke ce asalin ‘yar wahalar: Martanin jama’a bayan Safara’u ta kira ‘yan fim da ‘yan wahala a sabuwar wakarta ta ‘Kwalelenka’

A wasan sallah da tsohuwar jarumar Kannywood ta yi wato Safeeya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta yi tare da mawakin gambarar nan na Zaria, Mr 442 ya janyo cece-kuce, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Ganin bidiyon ya yi matukar hassala mutane da dama inda aka dinga ganin rashin dacewa tun daga shigarta har zuwa wakar har wasu su ke ganin kalmar Kwalelenka, batsa ce.

Sanin kowa ne cewa tarihin jarumar a masana’antar ba mai kyau ba ne har ake ganin dalilin kiran ‘yan fim da ‘yan wahala ya na da nasaba da cireta daga fim din.

‘Yan wahalan da ta dinga kiran ‘yan fim ya yi matukar daukar hankalin mutane sai dai kawo yanzu babu wata jaruma ko jarumi da ya yi magana akai.

Sai dai a bangaren ma’abota Facebook da TikTok ne abin ya sha bambam infa su ka dinga maganganu kala-kala da rubuce-rubuce.

Wani Comr Umar Uliyasu Danbaba ya yi wani rubutu a shafinsa na Facebook inda ya ce yanzu ya ke kara kallon maimaicin shirin Kwana Casa’in inda ya ganta da salihar fuskarta kafin ta sauya akala ta koma wata iri.

Ya bukaci a yi mata nasiha don ta gyara akalar rayuwarta kafin abinta ya kara tabarbarewa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe