22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wasu ɓata gari sun cinnawa wani matashi wuta saboda canjin N100

LabaraiWasu ɓata gari sun cinnawa wani matashi wuta saboda canjin N100

Ana zargin wasu ‘yan acaɓa da cinnawa wani matashi wuta a jihar Legas. Shafin LIB ya rahoto

Matashin mutumin mai suna David, an yi masa dukan tsiya sannan aka cinna masa wuta wacce tayi sanadiyyar ajalin sa.

Ana zargin matashin sun samu saɓani da wani ɗan acaɓa

Ana zargin cewa David ya samu saɓani ne da wani ɗan acaɓa kan canjin naira 100. Hakan ya sanya faɗa barkewa tsakanin David da ɗan acaɓan. 

Sauran abokan aikin ɗan acaɓan sun shiga cikin rigimar inda su ka yiwa David dukan tsiya har sai da ya sume.

David, yana kan hanyar sa ta komawa gida daga wajen shaƙatawa lokacin da lamarin ya auku a yankin Lekki Phase 1, jihar Lagos. 

An saka bidiyon lamarin a shafin Twitter

Bidiyon lamarin da aka saka a shafin Twitter ya nuna David a kwance a ƙasa da tayar mota na ci a jikin sa. Sannan mutanen da su ka farmake sa su ka sanya wa wutar man fetur, wanda hakan ya sanya wutar ta ƙaru.

David dai ya sha kashi ne tare da wasu abokan sa a hannun mutanen da har yanzu baa san ko su waye ba.

Abokan David, ma su suna Frank da Philip ana duba lafiyar su a wani asibiti da baa bayyana sunan sa ba.

Yadda matashi ya halaka abokin sa kan kuɗi $150 har lahira, ya kai kansa gaban hukuma

A wani labari na daban kuma, wani matashi ya halaka abokin sa har lahira kan kuɗi dala 150. Tuni dai matashin ya miƙa kansa zuwa gaban hukuma.

Wani mutum mai suna Oluwagbemiga Shogbola, mai shekaru 30 a duniya ya halaka abokin sa, Victor Olabiyo, kan kuɗi $150 (N61,950) na wani kasuwanci da su ka yi a ƙaramar hukumar Ikenne ta jihar Ogun.

Wanda ake zargin ya tuhumi abokin sa cewa ya cuce shi

Jaridar Punch ta rahoto cewa Shogbola, wanda aka fi sani da Oja ko Federal, ya zargi abokin sa da cutar sa ta hanyar tafiya da kuɗin gabaɗaya.

Hakan ya sanya cece-kucen da ke tsakanin su ya rikiɗe ya koma faɗa, wasu daga cikin abokanan su sun yi ƙoƙarin shiga tsakani amma abin yaci tura.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe