22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ko dai a hukunta makasan Deborah ko kuma in bar addinin musulunci, Keffe Arinola

LabaraiKo dai a hukunta makasan Deborah ko kuma in bar addinin musulunci, Keffe Arinola

Wata matashiya ta bayyana a dandalin TikTok inda ta bukaci gwamnati ta yi gaggawar hukunta wadanda su ka halaka Deborah Samuel wacce ta yi batanci ga ma’aiki, Alfijir Hausa ta ruwaito.

A cewarta, matsawar aka ki daukar hukunci akanta, to babu shakka za ta bar musulunci.

Matashiyar wacce bayerabiya ce, mai suna Keffe Arinola ta bayyana cewa, idan ba’a hukunta wanda suka halaka Deborah da ta yi wa Annabi Muhammad(SAW) batanci a Sokoto ba, zata yi gaggawar fita daga musulunci.

Ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok inda ta ce kisan da akawa Deborah ya sabawa koyarwar addini.

An birne gawar Deborah Samuel, ɗalibar da tayi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW)

An birne gawar ɗalibar nan Deborah Samuel, wacce aka halaka a kwalejin ilmin Shehu Shagari da ke a jihar Sokoto kan laifin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta Manzon Allah, Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata gareshi).

An birne Deborah Samuel a mahaifar ta

Jaridar TheNation ta rahoto cewa an birne Deborah Samuel ne a mahaifarta, da ke a garin Tunga Magajiya, cikin ƙaramar hukumar Rijau, a jihar Neja.

An dai birneta ne da misalin karfe 6:30 na yamma a maƙabartar mabiya addinin Kirista dake Tunga Magajiya.

Matasan garin sun ƙi bari a birne ta da farko

Da farko matasan garin Tunga Magajiya sun ki amincewa da a birneta inda su ka haƙiƙance cewa gwamnatin jihar Sokoto ya kamata ta ɗauki nauyin bikin birne ta, amma iyayen ta su ka ce lallai ayi mata jana’iza.

Sai dai kawun ta Emmanuel Maaji, wanda Fasto ne a cocin ECWA, ya jagoranci birne ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe