23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An birne gawar Deborah Samuel, ɗalibar da tayi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW)

LabaraiAn birne gawar Deborah Samuel, ɗalibar da tayi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW)

An birne gawar ɗalibar nan Deborah Samuel, wacce aka halaka a kwalejin ilmin Shehu Shagari da ke a jihar Sokoto kan laifin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta Manzon Allah, Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata gareshi).

An birne Deborah Samuel a mahaifar ta

Jaridar TheNation ta rahoto cewa an birne Deborah Samuel ne a mahaifarta, da ke a garin Tunga Magajiya, cikin ƙaramar hukumar Rijau, a jihar Neja.

An dai birneta ne da misalin karfe 6:30 na yamma a maƙabartar mabiya addinin Kirista dake Tunga Magajiya.

Deborah Samuel
Deborah Samuel. Hoto daga jaridar TheNation

Matasan garin sun ƙi bari a birne ta da farko

Da farko matasan garin Tunga Magajiya sun ki amincewa da a birneta inda su ka haƙiƙance cewa gwamnatin jihar Sokoto ya kamata ta ɗauki nauyin bikin birne ta, amma iyayen ta su ka ce lallai ayi mata jana’iza.

Sai dai kawun ta Emmanuel Maaji, wanda Fasto ne a cocin ECWA, ya jagoranci birne ta.

Kalaman Deborah Samuel sun tunzura ɗaliban makarantar inda su ka cinna mata wuta bayan ta sha dukan tsiya.

Ɓatanci: Mutane sun fito zanga-zangar neman a sako waɗanda su ka halaka Deborah a Sokoto

A wani labari na daban mutane sun fito kan tituna a jihar Sokoto domin neman a sako waɗanda aka kama saboda kisan da aka yiwa Deborah Samuel, ɗalibar da tayi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW)

An samu hatsaniya a wasu sassan jihar Sokoto, yayin da masu zanga-zanga su ka fito kan tituna domin nuna adawar su kan kamen da aka yiwa wasu da ake zargin su da hannu akan kisan ɗalibar da ta yi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Deborah Samuel, wata ɗaliba yar aji biyu a kwalejin ilmi ta Shehu Shagari, ta rasa ran ta a hannun fusatattun ɗalibai bisa zargin ta zagi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Mutanen da suka fito zanga-zangar sun ɗaga alluna waɗanda akayi rubutu iri-iri kamar, “ku sako yan uwan mu Musulmai,” “Musulmai ba yan ta’adda bane,” da sauran su.

Tun kafin lokacin fara zanga-zangar, an tura jami’an tsaro wurare masu muhimmanci waɗanda su ka haɗa da fadar mai martaba Sarkin Musulmi dake cikin birnin Sokoto.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe