27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Gwamna ya tuɓe rawanin basarake saboda halartar taron PDP

LabaraiGwamna ya tuɓe rawanin basarake saboda halartar taron PDP

Gwamnan jihar Cross Rivers, Prof Ben Ayade, ya sauke basaraken Muri Munene na ƙasar Efut kuma sarkin Calabar South, Itam Hogan Itam, daga kan kujerar sa. Jaridar Punch ta rahoto.

Basaraken ya saɓawa doka

Basaraken ya saɓa wa sashi na 30 sakin layi na 3 na dokar masarautun jihar Cross Rivers ta hanyar zuwa taron jam’iyyar PDP na yankin Cross River ta kudu, inda aka marawa wani ɗan takarar gwamna, Arthur Jarvis Archibong, baya.

Haka kuma basaraken yayi zaɓe a taron sannan kuma ya sanya hannu a rajistar mahalarta taron.

Taron dai ana zargin cewa ya gudana ne a bisa jagorancin tsohon gwamnan jihar, Donald Duke.

An shawarci sarakuna su daina shiga lamuran siyasa

Sarkin ƙaramar hukumar Bakassi, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar, Etinyen Edet, ya shawarci sarakuna da su tsame hannayen su cikin lamuran siyasa.

Gwamnan ya bayar da umurnin janye shaidar sa ta zama basarake a wata takarda da aka tura masa ranar 11 ga watan Mayun 2022, wacce mai ba gwamnan shawara ta musamman kan harkokin masarautu, Mr Adoga Victor, ya rattaɓawa hannu.

Jihar Cross Rivers dai tana a yankin kudu maso kudu na Najeriya ne.

Matar wani babban basaraken Yarbawa ta musulunta

A wani labari na daban kuma, matar wani babban basarake a yankin Yarbawa ta karɓi addinin musulunci. Matar basaraken dai ta shigo addinin musuluncin ne a cikin watan Ramadan.

Olori Joyce Anene Balogun, matar Olubadan ɗin Ibadanland, Oba Lekan Mohood Balogun, ta ƙarbi addinin musulunci. Shafin LIB ya rahoto

Matar basaraken ta shiga addinin musulunci cikin watan Ramadan

Olori Joyce Anene Balogun ta ƙarbi addinin musulunci a lokacin wata lakcar watan Ramadan wacce aka gudanar a ranar Litinin 25 ga watan Afrilu, a babban filin masallacin idi na birnin Ibadan ƙarƙashin jagorancin honorabul Ibraheem Akintayo. 

Babban limamin jihar Oyo, Sheikh Abdul Ganiyy Abubakry Agbotomokekere I, ya tabbatar da labarin a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook, inda ya ƙara da cewa sabon sunan sarauniyar na yanzu shine Khadijah Mahood Lekan Balogun.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe