24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Alkali ya yi wa ma’aurata rangwame akan sata saboda rashin abinci, ya nema musu tallafi a kotu

LabaraiAlkali ya yi wa ma'aurata rangwame akan sata saboda rashin abinci, ya nema musu tallafi a kotu

Alkalin kotun shari’ar majistare ta Mombasa dake Kenya, Vincent Adet ya yi wa wata mata da ake tuhuma rangwame tare da mijinta bayan an kama su da laifin satar garin alkama, sannan ya sa an hada wa ma’auratan kudi don su siya kayan abinci, LIB ta ruwaito.

An zargi ma’auratan, Saumu Ali da Evans Odhiambo da satar fulawa mai kimar Ksh. 1,980 daga Grain Industries Ltd a ranar 13 ga watan Afirilu a yankin Shimanzi da ke Mvita, wanda ya ci karo da sashi na 268 babi na 1 a sashin jerin laifuka na 275.

Yayin sauraron karar a watan Afirilu, biyun da ake tuhuma sun amsa laifukansu, gami da bayyanawa kotu yadda su ka sace garin alkama don kulawa da ‘ya’yansu, wadanda su ka dau tsawon kwanaki babu abinci.

Ali ta bayyana yadda take aiwatar da ayyukanta na share-share, yayin da mijinta ya bukaci ta taimaka masa wajen daukar buhun garin fukawa daga wata mota da aka ajiye kusa da gurin.

Ta amince da cewa kawai ta yi satar ne don ta ciyar da kananan ‘ya’yantata, sannan ta roki ayi ma ta sassauci, tare da alwarin ba za ta sake sata ba.

A bangaren Odhiambo, ya ce a da shi mai sana’ar kyadi ne, amma ya rasa aikinsa ne bayan shugaban kasa Uhuru Kenyatta ya haramta sana’ar kyadi. Ya amince da cewa ya saci abincin ne don ciyar da kananan ‘ya’yansa.

A zartarwansa a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, shugaban kotun majistare, Vincent Adet ya yi rangwame ga wadanda ake zargin, bayan dubi da rahoton da jami’in bincike ya gabatar gaban kotunsa.

“A bangaren jinkan bil’adama, musamman wacce ake tuhuma ta farko, na yi dubi da yanayin da aka aikata laifin, sannan na tausayawa halin da ta ke ciki, tare da kananan ‘ya’yanta uku da ke karkashin kulawarta, sannan ba ta da wani hanyar samun kudi, A saboda haka ne na ke son mu siya ma ta buhun fulawa da nama a yau,” K24 TV ta yanki abun da Adet ya ce.

Alkali ya bukaci al’umma, ‘yan jarida da ma’aikatan kotu da ke wurin da su bada gudunmawar iya abunda su ke da damar badawa don siyawa ‘yaran Saymu abinci, inda ya fara bada nasa gudunmawar ta hanyar mika ma ta Ksh. 1000.

Na gaji da cin bakin duka a hannun matata a raba mu, magidanci a gaban kotu

Wani manomi, Williams Famuyibo, a ranar Laraba ya bukaci wata kotun Mapo mai darajar farko da ke Ibadan da ta raba aurensa da matarsa mai cuzguna masa, Sola saboda tana yawan jibgarsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Famuyibo, wanda ke zaune a Ibadan, ya ce a halin yanzu bazai cigaba da jure dukan da take nada masa ba.

“Na tsere daga gidana a watan Janairu.

“Ya mai girma mai shari’a, saboda irin hantarata da cin zarafina da Sola takeyi, a halin yanzu ina zama ne tare da ‘dan uwana.

“Maganar gaskiya, bana samun kwanciyar hankali saboda bata kula dani.

“Ina da ‘ya’ya biyar kafin in auri Sola a shekarar 1990, amma dukkansu na gurin ‘yan uwana saboda munayen halayen Sola,” a cewar Famuyibo.

Sai dai Sola bata halarci zaman kotun ba ko kuma ta turo da wakili duk da sammacin da aka kai ma ta.

Shugaban kotun, SM Akintayo, ya umarci mai bada sammaci da ya sanar da wacce ake kara ranar da za’a sake zaman kotu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe