27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ɓatanci ga annabi: An ƙona wata ɗaliba har lahira a kwalejin ilmi ta Shagari

LabaraiƁatanci ga annabi: An ƙona wata ɗaliba har lahira a kwalejin ilmi ta Shagari

An ƙona wata ɗalibar kwalejin ilmi ta Shehu Shagari a Sokoto bisa zargin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW), ranar Alhamis.

An halaka ɗalibar bisa zargin yin ɓatanci ga annabi

Ɗalibar wacce aka zarga da zagin Annabi Muhammad (SAW), tasha duka sosai wanda yayi sanadiyyar suman ta.

A wani bidiyo da aka wallafa a yanar gizo, matasa sun jefa mata ɗuwatsu, yayin da wasu su ka yi amfani da bulali wajen dukan ta.

A lokacin da ta faɗi ƙasa a sume, matasan sun sanya mata tayoyi kafin su cinna mata wuta.

Majiyoyi sun bayyana yadda lamarin ya auku

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ɗalibar mai suna Deborah tayi ɓatancin ne a wani dandalin manhajar Whatsapp.

Yan ajin ta su ka ƙirƙiri dandalin domin tattauna abubuwan da su ka shafi karatun su, a cewar wata majiya

Wani ya bayyana cewa an saka wani sharhi kan addini a dandalin ne, sannan a lokacin da Deborah ke sukar sharhin, sai tayi ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW)

Wani kuma ya ƙara da cewa ta yi ɓatancin ne lokacin da su ke rigima da wata ɗaliba a ɗakin kwanan ɗalibai.

An buƙace ta da ta bayar da haƙuri amma taƙi, hakan ya ƙara fusata mutane a kwalejin. Jami’an tsaron kwalejin sun samu sun kai ta zuwa ofishin su, sai dai ɗalibai sun fi ƙarfin su, inda daga bisani su ka cinna mata wuta. A cewar majiyar

Ɓatanci ga Annabi Muhammadu SAW ya ja an yankewa Soheil hukuncin kisa 

A wani labari makamancin wannan kuma, An yankewa wani magidanci dan shekara 30 mai suna Soheil hukuncin kisa sakamakon sakonnin da yake sanyawa a shafin sa na Facebook. Sakonnin an yi su ne domin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW ). 

Rundunar yan sandan juyin juya hali na kasar Iran wato (IRGS ) sune suka cafke Soheil din tun a watan Nuwambar shekarar 2019 tare da matarsa. 

Arabi din yana da shafuka  wadanda aka bude da mabanbatan sunaye  har guda takwas a Facebook kuma dukkanin su ana batanci ne ga Annabi MUHAMMAD  (SAW). 
Ya kasance yana sanya abubuwa na rashin ladabi da kuma batanci ga Annabi, wanda kuma bai musa hakan ba. 

Wani dan karambani kuma dan bani na iya mai suna Eric Goldstein yace, zalunci ne a hukunta mutum domin ya sanya sako a shafin sa na Facebook, ko dan ya kalli wani abu a yanar gizo. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe