23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Abin al’ajabi: Ma’aikatan lafiya 11 a wani asibiti sun samu juna biyu a tare, 2 daga ciki rana ɗaya za su haihu

LabaraiAbin al'ajabi: Ma'aikatan lafiya 11 a wani asibiti sun samu juna biyu a tare, 2 daga ciki rana ɗaya za su haihu

Ma’aikatan lafiya mutum 11 masu aiki a wani asibitin birnin Missouri, suna ɗauke da juna biyu a lokaci ɗaya, inda biyu daga cikin ma’aikatan jinya daga cikin su, ake sa ran haihuwar su a rana ɗaya. Shafin LIB ya rshoto

A asibitin Liberty Hospital cikin Liberty, birnin Missouri, ma’aikatan jinya 10 da wata likita guda ɗaya suna ɗauke da juna biyu inda ake sa ran haihuwar su cikin watanni masu zuwa.

Da dama daga cikin su aiki ne a ɓangare guda

Da yawa daga cikin ma’aikatan lafiyan masu ɗauke da juna biyun, suna aiki ne a sashin unguwar zoma da kuma karɓar haihuwa.

Juna biyu
Abin al’ajabi: Maiaktan lafiya 11 a wani asibiti sun samu juna biyu a tare, 2 daga ciki rana ɗaya za su haihu. Hoto daga LIB

Darektan ɓangaren karɓar haihuwa, Nicki Kolling ya shaida wa Fox4 KC cewa:

Koda yaushe suna yin abubuwan su rukuni-rukuni, amma ba mu taɓa samun guda 10 a lokaci ɗaya ba, saboda haka wannan abin raha ne.

Ko a baya an taɓa samun irin haka

Wannan dai ba shine karon farko ba da wani asibiti ya samu ma’aikatan sa da dama na ɗauke da juna biyu a lokaci daya ba.

A shekarar 2019, ma’aikatan jinya 9 masu aiki a ɓangaren karɓar haihuwa a asibitin Maine Medical Center, suna ɗauke da juna biyu a lokaci ɗaya.

Haihuwar yarinyar a ranar 2/22/22 da karfe 2:22 a daki mai lamba 2 ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban kuma, wani abin al’ajabi ne ya faru inda aka haifi wata yarinya a ranar 2/2/22 da misalin ƙarfe 2:22

A ranar da ake kira “ranar biyu”, wata yarinya mai suna Juda Grace Spear ta bakunci duniya ne ta hanyar da wasu suka bayyana lamarin a matsayin abin al’ajabi. Ita dai yarinyar an haife ta a ranar 2/22/22 da karfe 2:22 na safe a dakin haihuwa mai lamba 2 a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Alamance a Arewacin Carolina, da ke kasar Amurka.

Haihuwar yarinya ya ja hankulan mutane a intanet, sun kwatanta haihuwan ta a matsayin abin mamaki
Kwanan wata da kuma lokacin da aka yi haihuwan su ne suka ja hankalin jama’a sosai a shafin yanar gizo inda mutane da yawa suke cewa ita wata aba ce mai albarka kuma abin al’ajabi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe