23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wani mugun mutum yayi garkuwa da ‘yar maƙocin sa mai shekaru 5, sannan ya halaka ta duk da ya karɓi kudin fansa

LabaraiWani mugun mutum yayi garkuwa da 'yar maƙocin sa mai shekaru 5, sannan ya halaka ta duk da ya karɓi kudin fansa

Jami’an tsaro sun kama wani mai suna Kabiru Abdullahi, bisa zargin yin garkuwa tare da kashe wata yarinya ‘yar shekara biyar, a jihar Bauchi. Jaridar Channelstv ta rahoto.

Hukumomi sun tabbatar da cafke masu laifin

Mai magana da yawun rundunar hukumar sibil difens mai suna Garkuwa Adamu, shine ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Litinin.

Ya bayyana cewa an kama Abdullahi mai shekaru 52, tare da wani Alhaji Yawale mai shekaru 45, biyo bayan
samun rahoton yin garkuwa da yarinyar mai suna khadija wacce ‘yar makocin Abdullahi ce, da suka samu, a ranar 23 ga watan Afirilu, a Sabon Garin Narabi dake ƙaramar hukumar Toro, a jihar Bauchi.

A binciken farko da aka gabatar, ya nuna cewa Abdullahin ya dauke Khadija ne a kofar gidan su, inda ya gudu da ita karkashin wata gada kusa da unguwar su, ya shake mata wuya, sannan ya saka ta a cikin buhu. ” Adamun ya bayyana

Ya kira mahaifin yarinyar, inda ya nemi kudin fansa, bayan tattaunawa akan kudin, sun yarda akan za’a biya Naira N150,000 domin a sake ta.

A fadar jami’in hukumar sibil difens, Yawalen ya karbi kudin kimanin N150,000, a ƙarƙashin wata bishiyar tsamiya a wani daji dake kusa da kauyen na Narabi.

An kwato wasu kayan laifi a hannun su

Ya ƙara da cewa, yayin cafke masu laifin:

Jami’an sun sami zunzurutun kudi har N42,000, kuɗin bogi dalar Amurka $200, layoyi, da kuma makullan mota iri-iri a matsayin shaida akan masu laifin. “

Bayan an zurfafa bincike, an samo cewa, an kashe Khadija tun a ranar 27 ga watan Afirilu, kuma an binne gawar ta a cikin ɗakin girkin gidan wanda ake zargi da aikata laifin.

Tawagar masu bincike sun je sun tono buhun da aka saka ta a ciki, inda suka garzaya da shi asibitin Toro, domin bincike, wanda daga baya likita ya tabbatar da mutuwar ta. ” Adamun ya fada.

Saurayi yasa anyi garkuwa da budurwar sa, ya ƙarbi kuɗin fansa miliyan 2

A wani labarin na daban kuma, jami’an ‘yan sanda ne ke neman wani saurayi ruwa a jallo bayan an haɗa kai da shi anyi garkuwa da budurwar da zai aura.

Saurayin mai suna Ahmed, ya haɗa kai da wani mutum mai suna Uchenna Daniels, domin yin garkuwa da budurwarsa mai suna Hannatu Kabri.

Mutanen biyu sai da su ka karɓi zunzurutun kuɗi har naira miliyan 2 kafin su sako Hannatu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe