28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kasar Indiya ta dakatar da matukan jirgi 9 da wasu ma’aikatan jirgi 32 saboda gwajin barasa

LabaraiKasar Indiya ta dakatar da matukan jirgi 9 da wasu ma'aikatan jirgi 32 saboda gwajin barasa
Indian flight attendant
Kasar Indiya ta dakatar da matukan jirgi 9 da wasu ma’aikatan jirgi 32 saboda gwajin barasa

Babban Daraktan Kula da Sufurin Jiragen Sama na Kasar Indiya, DGCA, ya dakatar da matukan jirgi 9 da ma’aikatan jirgin 32 saboda gwajin barasa da aka yi musu kafin tashin jirgin.
Gwajin ya gudana ne 1 ga watan Janairu har zuwa 30 ga watan Afrilu.

An samu barasa a cikin gwajin da aka musu

A cewar bayanan bincike da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Indiya ta fitar, ma’aikatan da abin ya shafa sun hada da matukin jirgi daya da ma’aikatan jirgi guda biyar na Go Air, matukan jirgi hudu da kuma ma’aikatan jirgin 10 na IndiGo.
Da matukin jirgi daya da ma’aikatan jirgi shida na kamfanin Spice Jet, sai matukin jirgin Air India Express, da ma’aikata hudu na Air Asia, dukkan su basu tsallake gwajin ba.

Sannan da matukin jirgi daya da ma’aikatan jirgi biyu na kamfanin Vistara, matukin jirgin Alliance Air daya da kuma ma’aikatan jirgin Air India biyar.
An bada sanarwar gwajin barasan ne tun kafin barkewar cutar COVID-19, an buƙaci duk ma’aikatan jirgin da su yi gwajin barasa kafin tashin jirage.

Barkewar cutar Corona ne ta hana gwajin tun kwanakin baya

Sakamakon barkewar cutar ta COVID-19 ne aka dakatar da gwaje-gwajen har na tsawon watanni biyu. Sai daga baya aka Aka dawo da gwajen bayan da aka janye takunkumin cutar Korona.

Ina sayar da wiwi ne saboda bana son yin sata, dillalin wiwi

Rundunar yan sanda ta jihar Kano, ta cafke wani dillalin wiwi da barayi ‘yan daba 128, tare da makamai da suke amfani da su wajen afkawa jama’a, a yayin bikin sallah da aka kammala, da kuma hawan Daba na sarki, a jihar. Jaridar Daily Trust ta rahoto

‘Yan sanda sun tabbatar da cafke masu laifin
Mai magana da yawun rundunar jihar
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine ya bayyana hakan a yayin da yake baje kolin masu laifin a sashen hukumar na Anti-Daba dake jihar ta Kano.

An kama yan daba, guda dari da ashirin da takwas, a tsakanin 2 da kuma 6 ga watan Mayu, a wannan shekarar ta 2022, yayin gudanar da hawan Idi, Japan Daushe, hawan Nassarawa’ da kuma ‘hawan Fanisau, wanda ake gudanarwa a fadin masarautun jihar guda biyar.

An kama masu laifin ne da muggan makamai, kayan maye da kuma kayayyakin sata.

Ya kara da cewa, an sami nasarar kama masu laifin ne da taimakon sauran hukumomin tsaro, yan sakai, da kuma sauran shugabannin al’umma. Hukumar tayi iya kokarin ta, domin tabbatar da yanayin lumana a yayin gudanar da bukukuwan karamar sallah.
Dillalin wiwi ya shiga hannu
Haka kuma, wani matashi mai suna Ayatullahi Abdulrahman, da aka kama shi da tabar wiwi, wanda dan unguwar Dorayi ne, ya shaida cewa, ya shiga sana’ar ne domin ya kare kansa daga shiga sace-sace.

Ga abin da ya ke cewa:

Yanzun nan na kammala kintsa tabar wiwi dina domin na fara siyarwa, kawai sai yan bijilanti suka kamani. Wiwi kadai nake siyarwa, kuma ina siyarwa ne kawai domin bana so in shiga sace-sace. Ina shan wiwi din da taba sigari, su kadai nake sha.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe