27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Wani mutum yayi wa ƙanwar matar sa mai shekaru 10 fyade, ya ɗora laifin kan giya

LabaraiWani mutum yayi wa ƙanwar matar sa mai shekaru 10 fyade, ya ɗora laifin kan giya

Ana tuhumar wani mutum ɗan acaba mai suna Godwin, da yin fyaɗe ga ƙanwar matar sa mai shekaru 10 a duniya a ƙauyen Kanshio, cikin ƙaramar hukumar in the Makurdi ta jihar Benuwai.

Jaridar Punch ta samo cewa an aiki yarinyar ne zuwa wani wuri lokacin da ta je wurin sayar da magani.

Mijin yayarta ya tafka mata fyaɗe

A yayin da ake mata tambayoyi, yarinyar da lamarin ya ritsa da ita, ta shaida wa mai sayar da maganin cewa mijin yayarta ya sadu da ita, inda ta ƙara da cewa da ta kai ƙorafi wurin yayarta sai ta manta kawai da lamarin.

An bayyana yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin ƙauyen, Patrick Adem, ya bayyana cewa matasan ƙauyen ne su ka bi mutumin har wurin da yake sannan su ka cafke shi, inda ya ƙara da cewa ɗan acaɓar ya amsa cewa ya aikata laifin.


Adem ya bayyana cewa:

Gabaɗaya lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar, kusan mutum 10 daga ƙauyen Kanshio, a ƙaramar hukumar Makurdi, su ka kawo Godwin zuwa gidan abokina. Sunan abokin nawa Mfe Shaminja, sirikin matar Godwin ne.

Sun bayyana cewa yarinyar taje siyan magani ne lokacin da ta ga wata ma’aikaciyar jinya, inda tayi mata ƙorafin tana fama da matsanancin ciwon ciki.

A lokacin da matar da tambaye ta abinda ya faru, ta bayyana cewa mijin yayarta yana saduwa da ita, sannan ta gayawa yayarta amma bata yarda da ita ba. Ma’aikaciyar jinyar ce ta tona masa asiri inda mutane su ka cafko shi a gidan sa.

Ya bayyana cewa ya je ya kwanta ne inda yaran ke barci inda anan ne lamarin ya auku. Ya ce sau ɗaya kawai lamarin ya auku, amma yarinyar tace ya sadu da ita yakai sai uku. Yarinyar ta kusa kai shekaru 10 a duniya.

An miƙa shi hannun hukuma

Wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Ukan Kurugh, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benuwai, sannan kuma an miƙa Godwin a hannun jami’an hukumar hana safarar mutane a jihar wato NAPTIP. 

Kwamandan shiyyar Makurdi na hukumar NAPTIO, Gloria Iveren-Bai, ta ce an cafke wanda ake zargin sannan kuma yarinyar na hannun hukumar su inda ta ke samun kulawa.

Ta bayyana cewa:

A ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu, hukumar NAPTIP reshen Makurdi, ta samu ƙorafi daga wani mutum wanda ya rubuto cewa wani Godwin Shagbaor yayi wa yarinyar sa mai shekaru 9 a duniya fyade

An ceto yarinyar da lamarin ya ritsa da ita inda aka kai ta asibiti domin yi mata gwaje-gwaje, kuma ana jiran sakamakon. Yanzu haka tana amsar kulawa.

Wanda ake zargi da aikata fyaden ya amsa cewa ya aikata laifin amma ya ɗora alhakin hakan akan giya. Wanda ake zargin yana kulle yayin da ake cigaba da gudanar da bincike

Ke duniya: Uba ya ɗirkawa ‘yar cikin sa mai shekaru 15 ciki bayan yayi mata fyaɗe

An cafke wani mutum mai shekaru 38 a duniya bisa laifin aikata fyaɗe ga ‘yar cikin sa mai shekaru 15 a duniya a jihar Ondo. Shafin LIB ya rahoto.

‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargin, Sunday Udoh, bayan yayi yunƙurin zubar da cikin da yarinyar ta samu bayan ya sadu da ita.

Udoh ya kai ɗiyar ta sa zuwa wani asibiti a Ile-Oluji, domin a zubar da cikin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe