29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

So gamon jini: Bidiyon mata da mijin da su ka kwashe shekaru 100 su na soyayya ya dauki hankalin jama’a

LabaraiLabaran DuniyaSo gamon jini: Bidiyon mata da mijin da su ka kwashe shekaru 100 su na soyayya ya dauki hankalin jama’a

Masoya biyu, Demian da Anastasia sun kwashe shekaru 100 a matsayin masoya kamar yadda bidiyonsu ya bayyana a yanar gizo.

Kamar yadda bidiyon na su ya nuna, sun hadu ne tun su na yara inda su ka so auren juna amma iyayensu su ka raba su, aka yi wa ko wanne auren dole.

Sai dai bayan shekaru da dama sun kara dawowa tare inda su ka ci gaba da soyayya daga nan ba su sake rabuwa da juna ba.

Soyayyar Demian da Anastasia ta dauki karni guda su na yin ta tare da nuna wa juna kauna, tausayi da kulawa.

Demian ya na da shekaru 106, yayin da matarsa, Anastasia ta ke da shekaru 102 kuma sun kwashe shekaru 100 su na soyayyar.

Sun fara soyayyar ne tun yarinta

Daga bidiyon wanda shafin YouTube na Afrimax English ta wallafa, sun ce iyayensu sun yi wa ko wannensu auren dole ne tun su na yaran.

Sai dai sun shiga damuwa kwarai lokacin da ba sa tare yayin da daga baya su ka dawo su ka jone da juna. Tun bayan sun yi auren, sun ci gaba da zama cike da kauna kuma har yau su na tsinkar fure.

Ga bidiyon:

‘Yan sanda sun yi ram da matar da ta halaka mijinta bayan ta gano ya na soyayya da wata budurwa

Wata mata ta na hannun hukuma bayan an kama ta dumu-dumi da laifin halaka mijinta bayan ya bayyana soyayyarsa ga wata matar, kamar yadda ‘yan sandan Texas na Amurka su ka bayyana hakan, LIB ta ruwaito.

Yayin bayani a ranar Asabar, 7 ga watan Mayu, Harris County Sheriff, Ed Gonzalez ya bayyana yadda aka kama Carin Stewart mai shekary 51, wacce ta bayyana cewa da kanta ta halaka mijinta bayan sun yi hayaniya akan soyayyarsa da wata mata.

‘Yan sandan da aka tura gidan sun ga yadda ya raunana sakamakon harsasai wadanda matarsa ta harbe shi, bayan ya sanar da ita cewa yana soyayya da wata mata, a cewar Gonzalez kamar yada Fox News ta ruwaito.

Gonzalez ya kara da cewa, take anan aka zarce da shi asabiti inda daga bisani ya mutu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe