24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

2023: Tunibu, Osinbajo da sauran ‘yan takara na cikin tsaka me wuya, yayin da APC ta fitar da sabbin ka’idodi guda 9

Labarai2023: Tunibu, Osinbajo da sauran 'yan takara na cikin tsaka me wuya, yayin da APC ta fitar da sabbin ka'idodi guda 9

Jamiyyar APC mai mulki ta fitar da wadansu dokoki guda tara, wadanda zasu jagoranci gudanar da zabukan shugaban kasa, yan majalisu da na gwamnoni, gabanin zaben, lokacin zaben da kuma bayan zabukan.

Jam’iyyar na son sulhuntawa a cikin gida

Daya daga cikin sharuddan shine, an haramtawa duk wani dan takara ya kai karar jamiyyar ko kuma wani dan jamiyyar, ba tare da ya nemi ayi sasanci daga cikin gida ba.

Kari akan wannan, dole ne kowanne dan takara a ko wanne mataki ya amince a rubuce, cewa zai karbi duk sakamakon da ya bayyana bayan zaben fidda gwani, kuma zai yi wa kowaye ya ci zaben fidda gwanin zaben 2023 aiki.

An bayyana sharuɗɗan

Jaridar The Nation, ta ruwaito cewa cikakken bayanin sharuddan yana kunshe a cikin fam din mai shafi 17, da kowanne dan takara ya saya, wadanda suke kamar haka :

1. Na yarda zanyi biyayya domin kiyayewa da kuma kariya ga dokokin jamiyyar APC, da na tarayyar Najeriya

2. Na yarda zanyi biyayya ga tanadin dokokin zaben fidda gwani na jamiyyar APC da kuma na hukumar zabe ta kasa.

3. Na yarda zanyi biyayya wajen sanya muradun jamiyyar APC sune a gaba akan muradun kai da kai

4. Da ni, da kungiyar yakin neman zabe na, da duk magoya baya na, munyi alkawarin goyawa duk wanda ta tabbata shine ya lashe zaben fidda gwani a jamiyyar APC, a babban zabe mai zuwa.

5. Na yarda zanyi biyayya cewa baza’a yi duk wani nau’i na rashin gaskiya ba kamar fadan jagaliya, kin zuwa taron mitin da aka gayyaci shi /ko ita, ba tare da wani mahimmin dalili ba; ko kuma ayi yunkurin canza sheka ta salon karya jamiyya, wanda yin hakan ka iya janyo rashin zaman lafiya a cikin jamiyyar, wanda kuma ya saba da burika da muradun jamiyyar.

6. A yarda da cewa baza’a bayar da duk wani gurbataccen batu akan jamiyya ba, ko fitar da wani jawabi da bai daceba ga jama’a, ba tare da anyi duk mai yiwuwa wajen sasanto a cikin gida ba.

7. A yarda cewa, baza’a kai jamiyya ko wani ma’aikacin ta kara kotu ba, akan wani aiki wanda hakkin ofishin jamiyya ne, batare bin duk wata maslaha da aka tanada a cikin gida ba

8. Na yarda ko yaushe na bi hanyar adalci, gaskiya da hadin kai a tsakanin yan takara da kuma daukacin yan jamiyya. Saboda haka ya Allah ka taimakeni.

9. Na yarda ba zan balle na ja wata zuga ba, ko na yi zabe na ni kadai ko na canja jamiyya a ko wanne mataki.

APC na son magance matsalar kai ƙararraki a kotu bayan zaɓe

Wadannan sharuddan, kandagarki ne da aka sanya domin ayi maganin kai komo na na kararraki da ake samu bayan gudanar da zabukan fidda gwani, wanda suke jefa jamiyya cikin rikici tun kafin babban zabe.

Matasa Bismillah: APC ta tsayar da N100m a matsayin kudin takarar shugaban kasa, N50m na gwamna

Jam’iyyar APC tsayar da N100 miliyan a matsayin kudin fom din takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 da ke kara matsowa, LIB ta ruwaito.

An tsayar da kudin ne ne yayin taron gaggawar na kwamitin zartarwar jam’iyyar, NEC wanda tayi a Abuja, yau 20 ga watan Afirilu.

Jam’iyyar ta sanar da kudin fom din takarar gwamna a N50 miliyan, majalisar dattawa N20 miliyan da majalisar wakilai N10 miliyan.

Inda jam’iyyar ta sanar da fara sayar da fom din takar a ranar Asabar, 23 ga watan Afirilu

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe