24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Hotunan shanu su na gararamba a titi bayan ‘yan ta’adda sun banka wa tirelar da aka kwaso su wuta

LabaraiHotunan shanu su na gararamba a titi bayan 'yan ta'adda sun banka wa tirelar da aka kwaso su wuta

An ga shanu su na yawo a titin Jihar Anambra bayan an banka wa motar da aka yi lodinsu wuta a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu, LIB ta ruwaito.

Bidiyon yadda aka kona tirelar ya bazu a kafafen sada zumunta.

shanu
Hotunan shanu su na gararamba a titi bayan ‘yan ta’adda sun banka wa tirelar da aka kwaso su wuta

Daga bisanu an ga shanun sun fita daga tirelar yayin da su ka dinga yawo a titi.

Majiyoyi sun ce lamarin ya auku ne a titin Ezinifite zuwa Uga da ke karamar hukumar Aguata da ke Jihar Anambra da misalin karfe 8 na safiyar Lahadi.

Masu kare hakkin shanu sun kashe wani musulmi a kan zargin fasa-kwabrin shanu a Indiya

‘Yan kwanakin nan kafar yanar gizo ta karade da bidiyon wani musulmi da aka gan shi wasu wadanda suka ce su masu kare hakkin shanu ne suna dukansa har ya mutu, a garin Bihar. 
A rahoton kananan kafofi, sun ce an kashe shi kuma aka yi kokarin kona gawarsa, bayan sun yaryada mata fetur. A wani hoton kuma cewa aka yi, sun yaryada masa gishiri ne a jikin sa kafin su binne shi. 


Mamacin wanda aka bayyana a matsayin Mohamad Khaleel Alam, dan jam’iyyar Janata Dal ne daga gundumar Samastipur.

Yadda mamacin ya dinga rokon masu kare shanun su kyale shi

An gan shi a cikin bidiyon ya durkusa yana neman afuwa a gaban wani wanda ya nade hannu yana tsaye, inda yake rokon su da su saka shi ya tafi.

Makashin wanda ya rufe fuskarsa da kyalle a bidiyon, cikin rashin imani, ya tambayi mamacin da ya bayyana inda aka yanka shanun, sannan kuma ya fadi sunayen wadanda suke siyar da shanun. 

Haka kuma, sun tambaye shi sau nawa ya ci naman shanu a rayuwar sa, da kuma wanda ya baiwa ‘ya’yan sa suka ci. Sun kara da tambayar sa cewa ko Qur’ani ya bada damar cin naman shanu?  Inda rikitaccen mamacin ya ce a’a. 

Bidiyon wanda ya cika da kalaman nuna kiyayya, ya zagaya tare da wadansu cin zarafi da ake yi wa musulmai. Amma abin takaici, wani kurtun ‘dan sanda ya musanta zargin, inda yace kawai ana son karkatar da hankalin jama’a ne domin a danne batun kisan. 
A sakon sa na Twitter, shugaban adawa na Bihar Tejashwi Yadav, ya jaddada rashin jin dadin sa a kan lamarin. Da yake magana a sakon Twitter din da harshen Indiyanci, yace babban minista Nitish Kumar ne yake da alhakin bayani a kan abin da yake faruwa a Bihar. 
A ranar Juma’a, 19 ga watan Fabarairu, an tsinci gawar Khaleel din a bakin gabar kogin Burhi Kadak, inda aka birne shi a cikin yashi. 
Tun da farko, dangin mamacin sun shigar da rahoton batan ‘dan uwan nasu tun a ranar 16 ga watan Fabarairu. Amma sai da suka dinga samun kira daga wayar mamacin, inda ake tambayar su kudi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe