24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

‘Yan sanda sun yi ram da matar da ta halaka mijinta bayan ta gano ya na soyayya da wata budurwa

Labarai‘Yan sanda sun yi ram da matar da ta halaka mijinta bayan ta gano ya na soyayya da wata budurwa

Wata mata ta na hannun hukuma bayan an kama ta dumu-dumi da laifin halaka mijinta bayan ya bayyana soyayyarsa ga wata matar, kamar yadda ‘yan sandan Texas na Amurka su ka bayyana hakan, LIB ta ruwaito.

Yayin bayani a ranar Asabar, 7 ga watan Mayu, Harris County Sheriff, Ed Gonzalez ya bayyana yadda aka kama Carin Stewart mai shekary 51, wacce ta bayyana cewa da kanta ta halaka mijinta bayan sun yi hayaniya akan soyayyarsa da wata mata.

dauri
‘Yan sanda sun yi ram da matar da ta halaka mijinta bayan ta gano ya na soyaya da wata budurwa

‘Yan sandan da aka tura gidan sun ga yadda ya raunana sakamakon harsasai wadanda matarsa ta harbe shi, bayan ya sanar da ita cewa yana soyayya da wata mata, a cewar Gonzalez kamar yada Fox News ta ruwaito.

Gonzalez ya kara da cewa, take anan aka zarce da shi asabiti inda daga bisani ya mutu.

An garkamr Stewart a gidan gyaran halin Harris County kuma an fara tuhumarta da kisan kai.

Matar aure ta sa ‘yan daba sun sace ‘yar Adama ta Dadin Kowa, sun yayyanketa saboda tana soyayya da mijinta

Zahra’u Sale, wacce aka fi sani da Adama ta Dadin Kowa ta bayar da labari mai ban tausayi a shafinta na TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Gidan rediyon Premier da ke Kano ma sun kawo rahoton inda suka ce wata matar aure da kawarta sun dauko hayar ‘yan daba sun je sun dauke Fa’iza Ja’afar wacce ‘ya ce ga Adama suka tafi da ita wani kango suka yayyanke ta sannan suka ja mata kunne akan ta rabu da mijin matar.

An samu nasarar damke matar auren da kawarta yayin da ita kuma Fa’iza ta ke kwance a gadon asibiti tana samun kulawa daga raunukan da suka ji mata.

Adama ta wallafa bidiyon wannan rahoton a shafinta na TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta nuna sannan ta rubuta “Ku taya ni jaje”, inda cikin rahoton wakilin gidan rediyon ya ce sun samu zantawa da Fa’iza, mijin matar da kuma ita Adaman, ga cikakken rahoton.

Cikakken rahoto

Kamar yadda wakilin ya ruwaito, an gurfanar da mutane 4 a gaban kotun majistare da ke Dawakin Tofa bisa zarginsu da cin zarafin wata Fa’iza Ja’afar.

Wakilin gidan rediyon Premier ya fara da cewa:

“Da fari dai an zargi Sumayya Idris da hada kai da kawarta, Aisha Yunus wadanda suka yi hayar ‘yan daba suka kama Fa’iza suka kai ta wani wuri, suka yi mata duka tare da yankarta a wuri daban-daban a jikinta.

“An samu bayanai akan yadda Sumayya Idris ta zargi Fa’iza Ja’afar da yin soyayya da mijinta. Hakan yasa suka hada kai da kawarta Aisha Yunusa wadanda suka dauki hayar ‘yan daba don su koya mata hankali.

“Sai dai bayan da abin ya faru ne ‘yan uwan Fa’iza sun kai kara ofishin ‘yan sanda da ke Unguwa Uku, inda aka kama wadanda suka yi aika-aikar ciki har da wadanda suka aikata mummunan aikin har da wani Umar da Hussain.”

Kamar yadda wakilin gidan rediyon Premier ya shaida, duk wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

Alkalin kotun, Al-Qasim Danfillo ya yanke wa wadanda ake zargin biyan tarar dubu goma-goma a ko wanne laifi da suka aikata ko kuma daurin watanni uku uku, kenan idan an hada wata tara.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe