28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Shekaru 16 da aure ba haihuwa, ya rasu bayan watanni 3 da matarsa ta haifi tagwaye

LabaraiShekaru 16 da aure ba haihuwa, ya rasu bayan watanni 3 da matarsa ta haifi tagwaye

Wani dan Najeriya, Chinedu Njirinzu, ya rasu bayan watanni 3 da matarsa ta haifi tagywaye, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda bayanai su ka nuna, sun kwashe shekaru 16 da aure su na jiran haihuwa shi da matarsa amma Ubangiji bai kawo ba.

abu twins
Shekaru 16 da aure ba haihuwa, ya rasu bayan watanni 3 da matarsa ta haifi tagwaye

Dan uwan matar mamacin, Igwe Ihedioha ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 6 ga watan Mayun 2022 yayin da ya ke bayyana alhininsa.

Kamar yadda Igwe ya wallafa:

“Na rasa kalaman da zan yi amfani da su bayan mutuwar sirikina, Prince Chinedu Njirinzu (Skippo).

“Ya kaunaci ‘yar uwata kuma ya na ta ba ta kwarin guiwa tsawon shekaru 16 ba su samu haihuwa ba.

“Bayan watanni 3 kacal da Ubangiji ya amsa addu’o’insu ya ba su tagwaye (mace da namiji), Ubangiji ya amshe shi.”

Daga nan ya wallafa hoton mutumin.

Mata ku koyi kulawa da jiki: Namijin da ya fara daukar ciki a duniya ya koma cakaras bayan haihuwa ta 3

Ko kun taba jin labarin mutum na farko a duniya da ya taba daukar juna biyu?

Duk da bai yi kama da maganar da hankali zai dauka ba, amma da gaske ne, Legitnaijanews.com ta ruwaito.

A cewar wani mutum mai suna Thomas an haifesa a mace, amma tuntuni yasan da cewa ya so zama namiji, saboda haka yana da shekaru 20, ya fara allurar testosterone (sinadin kwayoyin halittar maza), wanda ya yi sanadiyyar bayyanar sajensa, kankantar masa da murya da rage masa mazantaka.

A shekarar 2012, ya yanke shawarar yanke nonuwansa, yayin da matarsa ta cire mahaifarta.

Amma a wannan lokacin, Thomas ya yanke shawarar barin al’aurarsa ta mata.

Duk da ta hanyar dashe aka sanya masa ‘da. Amma a halin yanzu yana warkewa bayan ya haifi ‘ya’ya uku.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe