28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Tsananin kishi ya sanya ɗalibin sakandire halaka tsohuwar budurwar sa a cikin aji

LabaraiTsananin kishi ya sanya ɗalibin sakandire halaka tsohuwar budurwar sa a cikin aji

Wani ɗalibi mai shekaru 19 a duniya ya shiga hannun hukuma bayan ya halaka tsohuwar budurwar sa mai shekaru 22 a duniya. Shafin LIB ya rahoto

Ɗalibin ya halaka ta saboda tayi watsi da soyayyar sa

Darektan binciken laifuka na ƙasar Kenya, ya bayyana cewa Toni Kiptoo mai shekaru 19, ɗalibin makarantar sakandire ta Keben, ya cakawa tsohuwar budurwar sa, Chelagat, wuƙa a gefen ƙirjin ta na hagu, inda ta mutu nan take bayan tayi watsi da soyayyar sa.

Malaman makarantar sun bayyana Chelagat a matsayin ɗaliɓa mai hazaƙa da ƙwazo sosai, wacce tayi fice sosai a darasin turanci.

Ya daɗe yana shirin halaka ta

Binciken da hukumomi su ka gudanar sun tabbatar da cewa Kiptoo ya daɗe yana kitsa yadda zai halaka Chelagat, inda ya rubuta mata kalmar ‘RIP’ a wani hoton ta da aka samu a cikin wajen ajiya na teburin sa daga baya.

Ya fusata bayan ya fahimci tayi sabon saurayi

An kuma samo cewa masoyan guda biyu sun kasance suna soyayya mara dadi kafn rabuwar su, sannan tuni Chelagat ta cigaba da rayuwar ta. Sai dai, Kiptoo ya kasa haƙura sannan ya fusata bayan ya gano cewa tsohuwar budurwar ta sa tayi sabon saurayi wanda har ya siyo mata sabuwar waya dalleliya.

Ga abinda bayanin hukuma yake cewa:

Wani ƙauye a yankin  Sosiot Kericho ya shiga jimami bayan wani ɗalibin aji uku a sakandire ya halaka budurwar sa bayan alaƙar su tayi tsami. Lamarin wanda ya auku da safe a makarantar sakandiren Keben, Tony Kiptoo mai shekaru 19, ya cakawa Irene Chelagat, mai shekaru 22, wuka a gefen ƙirjin ta na hagu na, inda ta mutu nan take bayan tayi fatali da soyayyar sa.

Kiptoo, wanda yaci alwashin ɗaukar ran Chelagat, ya ɗauki wuƙa daga gida sannan ya aikata wannan mummunan aikin kafin a fara darussan safe.

A cewar ‘yan ajin mamaciyar, Kiptoo ya fusata ne bayan ya gano cewa tsohuwar budurwar ta sa ta yi sabon saurayi, wanda har ya siyo mata sabuwar waya.

Sannan kuma, ɗalibin wanda ake zargin yana a kotu yayin da jami’ai ai cigaba da haɗa shaidun da za su gabatar akan shi.

Yadda matashi ya halaka abokin sa kan kuɗi $150 har lahira, ya kai kansa gaban hukuma

A wani labari na daban kuma, wani mutum mai suna Oluwagbemiga Shogbola, mai shekaru 30 a duniya ya halaka abokin sa, Victor Olabiyo, kan kuɗi $150 (N61,950) na wani kasuwanci da su ka yi a ƙaramar hukumar Ikenne ta jihar Ogun.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Shogbola, wanda aka fi sani da Oja ko Federal, ya zargi abokin sa da cutar sa ta hanyar tafiya da kuɗin gabaɗaya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe