27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ai ke ce asalin ‘yar wahalar: Martanin jama’a bayan Safara’u ta kira ‘yan fim da ‘yan wahala a sabuwar wakarta ta ‘Kwalelenka’

LabaraiKannywoodAi ke ce asalin 'yar wahalar: Martanin jama'a bayan Safara'u ta kira ‘yan fim da ‘yan wahala a sabuwar wakarta ta ‘Kwalelenka’

A wasan sallah da tsohuwar jarumar Kannywood ta yi wato Safeeya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta yi tare da mawakin gambarar nan na Zaria, Mr 442 ya janyo cece-kuce, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Ganin bidiyon ya yi matukar hassala mutane da dama inda aka dinga ganin rashin dacewa tun daga shigarta har zuwa wakar har wasu su ke ganin kalmar Kwalelenka, batsa ce.

Sanin kowa ne cewa tarihin jarumar a masana’antar ba mai kyau ba ne har ake ganin dalilin kiran ‘yan fim da ‘yan wahala ya na da nasaba da cireta daga fim din.

‘Yan wahalan da ta dinga kiran ‘yan fim ya yi matukar daukar hankalin mutane sai dai kawo yanzu babu wata jaruma ko jarumi da ya yi magana akai.

Sai dai a bangaren ma’abota Facebook da TikTok ne abin ya sha bambam infa su ka dinga maganganu kala-kala da rubuce-rubuce.

Wani Comr Umar Uliyasu Danbaba ya yi wani rubutu a shafinsa na Facebook inda ya ce yanzu ya ke kara kallon maimaicin shirin Kwana Casa’in inda ya ganta da salihar fuskarta kafin ta sauya akala ta koma wata iri.

Ya bukaci a yi mata nasiha don ta gyara akalar rayuwarta kafin abinta ya kara tabarbarewa.

Wani Abdul-hadi Sharada ya ce:

“Safara’u kwana chasa’in ta koma Dani, da kai da ita, duka Allah ya shirye mu. Amin.”

Fatima Kaita ta ce:

“Safa safa Safara’u. Kwalelen ku. Ja’ira tasha liqin ‘yan hansin hansin wurin yaran gidan gala. Allah ka shiryad da mu.”

Aliyu Umar M. Gumel ya ce:

“A rayuwata ban taba jin tausayin wata ‘yar fim har kokon rai na ba sai akan Safara’u Kwana Casa’in.”

Har ila yau a TikTok ma sun dinga caccakarta. Wasu su na cewa ta haukace. Inda wasu su ka dinga cewa ita ce ‘yar wahalar.

Wasu sun ce ma ba ta da abin da za ta nuna har ta yi wa mutane kwalele. Don an riga an haukata ta sannan ta zama wawuya.

Akwai wanda ya ke ganin cewa ita ce babbar ‘yar wahala. Don ba matsalar kowa ba ne don ta bar fim ta koma waka.

Bidiyon Safara’u ta Kwana Casa’in tana tikar rawa da wakarta ta ‘Kwalelenka’ maza su na mata manni bayan an cire ta a fim

Jaruma Safeeya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta shirin fim mai dogon zango na Kwana Casa’in tana shan caccaka ta ko ina bayan ta bar fim din inda ta koma yin waka.

Kamar yadda cikin kwanakin nan bidiyonta ya dinga yawo a kafar sada zumunta wanda ta hau kan wata wakarta mai suna “Kwalelenka”, kowa ya razana.

Mutane da dama sun dinga yi mata fatan shiriya tare da neman iyayenta ko kuma wasu da ke da iko da ita da su yi gaggawar dakatar da ita daga turbar da ta dauka.

Sai dai a jiya, ranar Laraba ta saki wasu bidiyoyinta da wata shiga ta kananun kaya tana rawa da waka bayan ta tara maza a wani wuri mai kama da shagalin sallah.

A bidiyon ta hau wakar ta ta mai suna “Kwalelenka wacce mazan su ka dinga yi mata amshi tare da lika mata kudade.

Nan da nan mutane su ka tafi karkashin bidiyon su ka dinga yi mata fatan shiriya har da masu cewa ta zama abin tausayi don wannan hanyar da ta dauka ba mai kyau bace.

A cikin wakar an ji baitin da ta ke cewa “na bar sana’ar wa ‘yan wahala”, da alamu ta hassala ne bayan cire ta daga fim, hakan ya sa ta ke yi wa ‘yan Kannywood habaici.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe