24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

‘Yan sanda sun cafke wani ɗan Najeriya da abokin harƙallar sa bisa damfarar mutum 13 zunzurutun kuɗi N27m a ƙasar Indiya

Labarai'Yan sanda sun cafke wani ɗan Najeriya da abokin harƙallar sa bisa damfarar mutum 13 zunzurutun kuɗi N27m a ƙasar Indiya

Yan sanda a birnin Ahmedabad na ƙasar Indiya sun cafke wasu mutum biyu ciki harda wani ɗan Najeriya bisa damfarar wasu mutum 13 zunzurutun kuɗi har  Rs 2.75 crore (N27m) da sunan safarar maganin gargajiya. Shafin LIB ya rahoto

‘Yan sanda sun samu nasarar cafke waɗanda ake zargin

‘Yan sanda sun bayyana cewa waɗanda ake zargin, Chinedu Anumole, mai shekaru 39 a duniya, mazaunin  Nallasopara a birnin Mumbai, da kuma Rakesh Kashyap, mai shekaru 37 a duniya, mazaunin Navi Mumbai, an cafke sun inda aka taso ƙeyar su zuwa birnin Ahmedabad a ranar Laraba 4 ga watan Mayu.

Wani mazaunin Ahmedabad ya shigar da ƙorafi a wurin mu cewa an mai talla a shafin sa na Facebook dangane da wani kamfanin ƙasar Poland mai buƙatar maganin gargajiya na ‘Anigra’

A cewar wani jami’in ɗan sanda. 

Waɗanda ake zargin sun bayar da kamashon kaso 20 sannan su ka siya lita ɗaya na maganin kan kuɗi Rs 1.18 lakh daga wurin sa. Bayan ya yarda da su, sai su shigar da odar maganin da yawa inda daga bisani su ka damfare shi Rs 8.18 lakh,” 

Mun ƙwace wayoyi hannu guda 6 da litoci da dama na maganin gargajiyan a hannun waɗanda ake zargin. Hanyar da su ke bi shine suna tuntubar mutane a ƙafafen sadarwa sannan su nemi da su yi harkar kasuwanci da kamfanin bogi na ƙasar Poland.

An kama dan Najeriyan da ke tatsar kudin matan Indiya da sunan zai aure su

A wani labari daban kuma, ‘Yan sanda sun yi ram da wani dan Najeriya, tare da abokan sa biyu a kasar Indiya, bisa zargin su da damfarar mata inda suke musu alkawarin aure, LIB ta ruwaito.

An kamo mazan guda uku, tare da wani dan Najeriyaa garin Ghaziabad da ke Uttar Pradesh bisa zargin su da yaudarar mata ta hanyar kulla soyayya da su a kafafan sada zumuntan zamani.

Ana zargin Arvind Verma, Prince Pandey da hada kai dadan Najeriyan mai suna Didier.

Takardar da rundunar ‘yan sanda ta fitar a ranar Juma’a 18 ga watan FabrairuN 2022, inda su ukun suke soyayya da mata a kafafan sada zumunta ta hanyar nuna su Indiyawa ne amma ba sa zama a kasar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe