Masu nazari akan al’amuran Kannywood sun yi ittifaki akan cewa ba a taba samun shekarar da ‘yan masana’antar su ka kwashe zuwa Saudiyya ba kamar wannan shekarar, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.
Hatta al’amuran masana’antar sun tsaya cak saboda yadda yawancin jaruman su ka kwashe su ka tafi kasa mai tsarki.
Akalla jarumai 40 da doriya ne su ka samu zuwa ummara wannan shekarar wanda har Ali Jita dai da ya wallafa a shafinsa.
Kamar yadda ya rubuta a shafinsa:
“Kamar fa mu da muka rage a Kano ba mu da yawa. Kowa yana saudiyya. Ku rika sa mutanenmu na Saudiyya a addu’a.”
Sai dai wani abu da za a iya cewa shi ne musabbabin zuwan ‘yan fim saudiyya shi ne, sanin kowa ne cewa ba yau su ka fara kasar ba don su kan je har aikin hajji.
Sannan su kan fita yawon shakatawa daga nan su yada zango a Saudiyya sannan su biya Dubai don siyayya daga nan su karkato gida.
A wannan shekarar kuwa ana ganin kamar zuwan nasu yana da alaka da yadda aka kwashe shekaru 2 ba a je kasar ba hakan ya sa su ka yi tururuwar.
Sanin kowa ne cewa a shekarar 2020, Corona ta hana kowa zuwa kasar sannan a shekarar 2021 an tsaurara matakan kariya wanda sai a wannan shekarar ne aka saukaka matakan.
Akwai yuwuwar hakan ne ya sa mutane su ka dinga cincirindon zuwa kasar.
Wadanda su ka samu damar halartar sun hada da Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Shamsu Dan’iya, Ado Gwanja, Adego, Suleiman Costume, Sani Candy, Mustapha Naburaska, Ibrahim Sharukan, Ahmed Ali Nuhu, Baballe Hayatu da sauransu.
A bangaren mata kuwa akwai Hadiza Gabon, Nafisat Abdullahi, Aisha Tsamiya, Halima Atete, Hannaty Bashir, Teema Yola, Rahama Sadau, Ummi Gayu, Ummi Rahab, Hafsat Idris, Momi Gombe da sauransu.
Sai dai yayin da malamai su ke jan kunne, sun nuna cewa kamar isgilanci ne daukar Selfie yayin da mutum ya je gaban harami ya na addu’o’i.
Yawancin ‘yan fim warin baki gare su, Jaruma Angela Eguavoen ta fasa kwai
Fitacciyar jarumar fina-finan kudu, Angela Eguavoen ta ce abokan sana’arta maza suna fama da warin baki, Pressinformant.com ta ruwaito.
Yayin tattaunawar da akayi da ita a ranar Asabar, ta bayyana cewa yayin da ake umartar ta da sumbatar abokan aikin ta idan suna shirya fim, tana haduwa da masu warin baki. Amma ta ce akwai wasu masu tsafta.
Kamar yadda ta kada baki ta ce:
“Akwai jarumai maza da dama da ban ji dadin sumbatar su ba. Idan ka hadu da mai warin baki gaskiya babu dadi. Na fuskanci irin hakan kwarai da gaske.
“Har ila yau akwai masu tsafta sosai da na yi aiki da su yayin shirya fina-finai. Gaskiya hakan ya kayatar da ni.”
Yayin da aka tambaye ta nata ra’ayin dangane da mata masu amfani da asiri wurin mallakar namiji, ta ce hakan yana faruwa a masana’antar.
Kamar yadda Angela tace:
“Amfani da asiri wurin mallakar namiji babban kuskure ne. Hakan yana nuna tsananin rashin sanin ciwon kai. Ba zan taba ba wata shawarar aikata hakan ba. Duk bala’i kada mace ta yi amfani da asiri wurin rike namiji. Idan ta kwantar da hankalin ta sai ta hadu da wanda ya fi shi.”
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com