27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bidiyon Safara’u ta Kwana Casa’in tana tikar rawa da wakarta ta ‘Kwalelenka’ maza su na mata manni bayan an cire ta a fim

LabaraiKannywoodBidiyon Safara’u ta Kwana Casa’in tana tikar rawa da wakarta ta 'Kwalelenka' maza su na mata manni bayan an cire ta a fim

Jaruma Safeeya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta shirin fim mai dogon zango na Kwana Casa’in tana shan caccaka ta ko ina bayan ta bar fim din inda ta koma yin waka.

Kamar yadda cikin kwanakin nan bidiyonta ya dinga yawo a kafar sada zumunta wanda ta hau kan wata wakarta mai suna “Kwalelenka”, kowa ya razana.

Mutane da dama sun dinga yi mata fatan shiriya tare da neman iyayenta ko kuma wasu da ke da iko da ita da su yi gaggawar dakatar da ita daga turbar da ta dauka.

Sai dai a jiya, ranar Laraba ta saki wasu bidiyoyinta da wata shiga ta kananun kaya tana rawa da waka bayan ta tara maza a wani wuri mai kama da shagalin sallah.

A bidiyon ta hau wakar ta ta mai suna “Kwalelenka wacce mazan su ka dinga yi mata amshi tare da lika mata kudade.

Nan da nan mutane su ka tafi karkashin bidiyon su ka dinga yi mata fatan shiriya har da masu cewa ta zama abin tausayi don wannan hanyar da ta dauka ba mai kyau bace.

A cikin wakar an ji baitin da ta ke cewa “na bar sana’ar wa ‘yan wahala”, da alamu ta hassala ne bayan cire ta daga fim, hakan ya sa ta ke yi wa ‘yan Kannywood habaici.

Ga bidiyon wanda ta sanya a shafinta:

LabarunHausa.com ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a karkashin bidiyon nata:

Official_mrs_Akanji ta ce mata:

“Kyakkyawa ce ke, don Allah kada ki yi wa kanki haka. Akalla za ki iya waka amma wannan hanyar ba mai kyau ba ce.”

Officialpharouq ya ce:

“Wannan ‘yar titi ce.”

UsmanKabiru14 ya ce:

“Wlh wlh ina tausaya miki saboda idan kanwata ce na gani a wannan halin ba zan ji dadi ba. Allah ya shirye mu gaba daya.”

Jerin jaruman Kannywood 12 da su ka yi soyayya da junayensu amma ba ta kai su ga aure ba

Mutane da dama basu da masaniya game yadda jaruman Kannywood sukayi soyayya cike da nishadi tsakanin wasu maza da mata ba.

Da sannu zamu bayyana muku jaruman Kannywood guda 12 da sukayi soyayyar gaskiya tsakaninsu, Tashar G24 TV ta YouTube ta ruwaito.

  1. Jarumi Lawan Ahmed da Fati Muhammed

Jarumi Lawan Ahmed a wata tattaunawa da BBC Hausa ta taba yi da shi a shirinsu na Daga Bakin Mai Ita, ya bayyana cewa sun taba soyayya da Fati Muhammad amma Allah bai yi zasu yi aure ba.

lawan and fatee
  1. Soyayyar Hadiza Gabon da Naziru Ahmed

Duk da dai mawakin yana yawan kushe ‘yan fim din inda ya ke yawan cewa ba su da tarbiyya. Amma a wani bidiyo da ya yi yayin takaddama da jaruman ya ce ya taba soyayya da Hadiza Gabon amma ba kowa ya san da hakan ba.

hadiza gabon da nazir


Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe