24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Ka koma Islamiyya: Jarumi Ibrahim Sharukan ya sha caccaka bayan bayyanar bidiyon karatun Qur’aninsa cike da kura-kurai

LabaraiKannywoodKa koma Islamiyya: Jarumi Ibrahim Sharukan ya sha caccaka bayan bayyanar bidiyon karatun Qur’aninsa cike da kura-kurai

Fitaccen jarumin Kannywood kuma mai shirya sha’ani, Malam Ibrahim Sharukan ya sha caccaka bayan ya saki wani bidiyonsa wanda ya ke karatun Qur’ani mai girma.

A bidiyon an ji yadda ya ke ta karatu cike da kura-kurai kuma alamu na nuna cewa da gaske ya ke karatun ba don ya bai wa kowa dariya ba.

sharukhan
Ka koma Islamiyya: Malam Ibrahim Sharukan ya sha caccaka bayan bayyanar bidiyon karatun Qur’aninsa cike da kura-kurai

Ya yi bidiyon ne bayan ya saki wani na daban wanda ya ce sun je Umrah inda su ka yi dawafi musamman don Ubangiji ya saka musu kalaman da Sarkin Waka ya yi akan su na batanci.

Wannan bidiyon na sha ya sa mutane su na ta cewa dakyar idan yawancin jaruman Kannywood ba sa fama da jahilci ta fannin addini.

Idan mutum ya saurari karatun zai gane cewa tun daga Bismillah ya fara tafka kuskure har zuwa karshen karatun.

Ya kai mintuna 20 da doriya yana yin bidiyon kamar yadda shafin BVC ya saki a Facebook. Ga bidiyon:

https://fb.watch/cNXRAj1vvB/

LabarunHausa.com ta tattaro wasu daga cikin tsokacin mutane karkashin wallafar.

Wata Mariya Muazu ta ce:

“A koma islamiyya ,akwai gyara.Allah ya bamu ikkon gyara gaba daya.”

Bello Taba ya ce:

“Muna rokon Naziru Sarkin Waka ya dubu Allah da Manzon shi kadda ya kalli halin ‘yan Kannywood ya temaka ya bude masu Islamiyya kafin jahilci ya kashe su.”

Aleeyu Ismaeel ya ce:

“Kayiwa Allah sarki kabude islamiya Dan girman Allah ka ceto batattu izuwa ga shiriya.”

Muhammad Aminullahi ya ce:

“Subhanallahi. Tabbas Allah yana da haquri. Babu wani Sarkin da za’a canza masa magana irin haka be dauki mataki nan take ba sai sarki Allah. Allah mungode.”

Zainab Uzairu Umar ta ce:

“Subhanallah kuma ahaka kke sallah har wasu suke ce maka malam Dan Allah ka koma islamiyya ko izu 1 ka samu plx kodan ka samu gyara acikin sallah. Wlh ka bani tausayi.”

Wasu ‘yan Kannywood sun yi wa Sarkin Waka Dawafi suna fatan Allah ya yi musu sakayya akan kalamansa

Tsugunne bata kare ba dangane da rigimar Sarkin Waka da Nafisat Abdullahi, yayin da maganganu suke ta bullowa ko ta ina, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Wasu daga cikin ‘yan fim din sun goya masa baya yayin da wasu suka dinga caccakarsa musamman a Facebook da TikTok.

Yawancin wadanda suka je Saudiyya yin Ummara sun yi shiru ba tare da sun tofa komai ba ko kuma yin martani akan maganimun da ya yi.

Jarumi Malam Ibrahim Sharukhan, Suleiman Costome, mai haska dandali, Sani Candy da kuma Jarumi Adebo duk sun bayyana cewa sun yi dawafi inda suka kai kukansu ga Allah akan munanan maganganun da Sarkin Waka ya yi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe