27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Duk da bayyanar bidiyon tsiraicin Ummi Rahab, ko kadan Lilin Baba bai kadu ba saboda tsabar fahimtar junansu, Yayanta

LabaraiKannywoodDuk da bayyanar bidiyon tsiraicin Ummi Rahab, ko kadan Lilin Baba bai kadu ba saboda tsabar fahimtar junansu, Yayanta

An samu bayanai akan wani bidiyon jaruma Ummi Rahab wanda ta ke zaune akan gado tana ta zuba wanda ta ke sanye da wani gajeren wanda da wata riga mai kama da shimi wanda ya dinga yawo a kafafen sada zumunta.

Tashar Tsakar Gida ta ruwaito yadda mutane da dama sun dinga bayyana ra’ayoyinsu akan bidiyon wanda yawanci su ke ganin hakan ya na daya daga cikin sharrin makiya da mahassada da ke ganin ta kusa aure su na son su watsa lamarin.

ummmii
Duk da bayyanar bidiyon tsiraicin Ummi Rahab, ko kadan Lilin Baba bai kadu ba saboda tsabar fahimtar juna, Cewar yayanta

Wannan ya na daya daga cikin tarin dalilan da ya sanya jarumai su ke boye wadanda za su aura ko kuma batun aurensu har sai lokacin ya zo daf sannan su bayyana.

Hakan ya sa Tashar Tsakar Gida ta tuntubi Yasir Ahmad, wanda ya ke matsayin wa kuma mai kula da Ummi Rahab wanda ya yi karin haske akan bidiyon.

Kamar yadda Yasir ya bayyana, wannan sharrin mahassada ne kuma bidiyon ba sabon bidiyo bane kuma an dauke shi ne tun kafin ta dawo harkar fim.

Ya ci gaba da cewa ko shi da ganin bidiyon ya shi shekara daya. A cewarsa a dauki bidiyon ne a dakin wata amarya a family din su lokacin ana sha’ani.

A cewarsa ko lokacin da su ka ga bidiyon sun bibiyi wacce ta dauka inda ta nuna alhininta akai kana ta ce ta sayar da wayarta ne, ta yuwu daga nan ne bidiyon ya yadu.

Yayin da aka tambayi Yasir idan bidiyon ya tayar wa wanda zai auri Ummi da hankali, ya shaida cewa ko kadan bai kadu ba saboda akwai fahimtar juna sosai tsakaninsa da Ummi.

Yayin da aka tambaye shi idan batun aurenta yana nan inda ya tabbatar da cewa tabbas auren yana nan kuma an dade da da rana. Da zarar ta dawo Ummara da kyar a kara mako 2 ba a yi bikin ba.

An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Yayin da mutane suke ta jita-jita da surutai akan cewa ‘yan fim ba sa auren junan su, Lilin Baba da Ummi Rahab zasu karya wannan rantsuwar ta’yan fim ba sa auren juna, don yanzu haka an sanya ranar auren su.

A rana Juma’a, 4 ga watan Maris Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa batun sa ranar auren nasu.

Yanzu haka duk wasu shirye-shirye sun kankama akan cewa Lilin Baba zai angwance da amaryarsa, Ummi Rahab bayan sallah mai zuwa.

Tashar Tsakar Gida ta samu labari akan cewa manyan jarumai kamar Ali Nuhu ne suka shige wa mawakin gaba akan neman auren auren Ummi kuma an ba su auren ta.

Ba don wani akasi da aka samu ba da tuni an daura auren kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta tattauna da daya daga cikin waliyyan amarya, Yasir Ahmad wanda ya tabbatar da cewa za a daura auren bayan sallah.

Baya ga hakan, akwai wani bidiyo da jaruma Umma Shehu ta wallafa wanda ya kara tabbatar da hakan wanda aka ga Lilin Baba da Amaryar tasa cike da farin ciki, a karkashi ta sanya “our next couple”.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe