23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Shugaban kasa Buhari ya bada haske akan wanda zai gajeshi 

LabaraiShugaban kasa Buhari ya bada haske akan wanda zai gajeshi 


Yayin da zaben Shugaban kasa na shekarar 2023 ke karatowa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin magana akan wanda zai gajeshi. 


Idan za’a iya tunawa, shekarar da ta gabata shugaban yayi wata magana a kafar talabijin, cewa shi bai damu da waye zai gajeshi ba, bayan ya sauka daga mulki. 

buhari
Shugaban kasa Buhari ya bada haske akan wanda zai gajeshi 


Daga baya kuma, sai yace duk da cewa yana da dan takara, amma yana jin tsoron bayyana shi saboda

A wajen sallar Idi Buharin ya bada hasken

Da yake magana a wajen sallar Idi da aka gabatar a Mambila Barrack dake gidan gwamnati a Abuja ranar Litinin, Buharin ya dada jaddada kokarin sa na ganin an sami sahihin zabe mai inganci. 

 Da aka matsa masa ya fadi wanda zai mekawa mulki, bayan ya kammala, sai Buharin yace “wanda ‘yan Nageriya suka zaba”. 

Buhari yayi kira ga jami’an tsaro baki dayan su


Haka kuma, shugaban ya nemi shugabannin hukumomin tsaro, da su nemo duk inda  ‘yan ta’adda suke, su murkushe su. 


“Zamu ci gaba da tabbatarda kakkabe yan ta’adda daga muhallan jama’a, musamman yanzu da za’a shiga damuna , saboda manoman mu su sami shiga gonakin su domin samar da  abinci.


“Shugabannin jami’an tsaron sojoji, na kasa na ruwa na sama da kuma shugaban rundunar yan sanda na kasa, da sauran su, duk suna sane  akan lamarin tsaro, aikin su ne, su gano duk inda  ‘yan ta’adda suke domin su murkushe su.” Buharin ya fada.

Ni zan gaji kujerar shugaba Buhari a shekarar 2023 – Gwamna Yahaya Bello

Gwamnan Yahaya Bello na jihar Kogi, ya tabbatar da cewa tabbas shine zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da za a gabatar a shekararr 2023.

Gwamnan ya bayyana hakane a ranar Litinin a lokacin da yake hira da gidan talabijin na Arise TV, wanda jaridar The Nation ta nada.

A cewar gwamnan, ya na da duka kwarewa da cancanta ta zama shugaban kasar Najeriya.

“Da ikon Allah idan aka rantsar dani a matsayin shugaban kasar Najeriya bayan Buhari a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023, Najeriya za ta samu sauki ta kowanne bangare,” cewar shi.

Dangane da kiran da wasu matasan Najeriya ke yi don ya fito takarar shugaban kasa a 2023, ya ce:

“A lokacin dana shiga a ofis a shekarar 2016, na riski jiha wacce ta samu rabuwar kai na addini, al’ada, da yare.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe