28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Jerin jaruman Kannywood 12 da su ka yi soyayya da junayensu amma ba ta kai su ga aure ba

LabaraiKannywoodJerin jaruman Kannywood 12 da su ka yi soyayya da junayensu amma ba ta kai su ga aure ba

Mutane da dama basu da masaniya game yadda jaruman Kannywood sukayi soyayya cike da nishadi tsakanin wasu maza da mata ba.

Da sannu zamu bayyana muku jaruman Kannywood guda 12 da sukayi soyayyar gaskiya tsakaninsu, Tashar G24 TV ta YouTube ta ruwaito.

  1. Jarumi Lawan Ahmed da Fati Muhammed

Jarumi Lawan Ahmed a wata tattaunawa da BBC Hausa ta taba yi da shi a shirinsu na Daga Bakin Mai Ita, ya bayyana cewa sun taba soyayya da Fati Muhammad amma Allah bai yi zasu yi aure ba.

lawan and fatee
  1. Soyayyar Hadiza Gabon da Naziru Ahmed

Duk da dai mawakin yana yawan kushe ‘yan fim din inda ya ke yawan cewa ba su da tarbiyya. Amma a wani bidiyo da ya yi yayin takaddama da jaruman ya ce ya taba soyayya da Hadiza Gabon amma ba kowa ya san da hakan ba.

hadiza gabon da nazir
  1. Sani Danja da Maryam Jan Kunne.

A fina-finan baya ana yawan nuna su tare suna fitowa amma ba kowa ya san sun taba soyayya ba.

Sai dai a wata hira da BBC Hausa ta yi da Maryam, ta bayyana cewa sun taba soyayya da Sani Danja amma Allah bai yi za su yi aure ba.

sani danja da maryam
  1. Mustapha Naburaska da Hadiza Kabara

Naburaska fitaccen jarumin wasan barkwanci ne wanda yayin da aka yi hira da shi ya bayyana cewa yana da niyyar auren Hadiza Kabara.

hadiza kabara da naburaska
  1. Soyayyar Adam Zango da ‘yan matan Kannywood guda 3, Nafisat Abdullahi, Fati Washa da Ummi Rahab.

Lokacin da Adam da Nafisat suka yi soyayya tana yawan nuna masa soyayya a ko yaushe.

Sannan a wata hira da aka yi da jarumin ya taba cewa yana da burin auren Nafisat Abdullahi da Fati Washa.

Sannan yayin da aka samu wani rikici tsakanin Ummi Rahab da Zango, dan uwanta ya bayyana cewa jarumin ya so aurenta amma daga bisani ya janye jiki.

adam zango da 3 babes

Jerin matan Kannywood 6 da aurensu ya mutu suka dawo harkar fim dumu-dumu

A shekarar nan an samu mace-macen aure daban-daban a shekarar 2022 musamman a masana’antar Kannywood.

Sai dai sukan ce a ko yaushe kuma a ko ina aure yana mutuwa amma tasu ta fi fitowa kasancewar sanannu ne.

  1. Zarah Diamond

Fitacciyar jarumar ta yi aure ne a shekarar 2021 wandaya kasance na sirri don bata sanar da mutane da dama ba, Arewa Package TV ta ruwaito.

Sai dai daga baya aka samu labarin mutuwar auren nata wanda daga baya ta dawo ta ci gaba da harkokinta da wallafe-wallafenta a kafafen sada zumunta.

  1. Rahama Hassan

Jaruma Rahama ta yi aure a shekarar 2017 ne, sai dai ta bayyana a wani bidiyo wanda Furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda ya wallafa na ‘yan kungiyar 13 times 13 suka yi.

Wannan bidiyon ne ya tabbatar da cewa aurenta ya mutu saboda sun yi hoton gab da gab kuma shigarta bata yi kama da ta matan aure ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe