23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wani malamin tsubbu ya shiga hannun hukuma bayan ya yi damfarar N5.475m

LabaraiWani malamin tsubbu ya shiga hannun hukuma bayan ya yi damfarar N5.475m

Rundunar ‘yan sanda jihar Ogun ta yi ram da wani malamin tsubbu mai suna Abdulsalami Yakub bisa zarginsa da damfarar al’umma, LIB ta ruwaito.

An kama wanda ake zargin ne bayan shigar da korafi da wata Rukayat Ibrahim ta yi ga kwamishinan ‘yan sandan, inda ta zargeshi da damfararta da kanwarta, Olueaseun Ibrahim, jimillar kudi N5.475 miliyan.

Rukayat ta ce Yakub ya musu karyar cewa zai ma diyarta maganin sammu.

An gano kan dodo, layu da tukwanen tsafi bayan an bincike gidansa.

Haka zalika, kakakin ‘yan sanda jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shawarci ‘yan Najeriya da su zama masu taka tsan-tsan da wanda za su je mawa da nufin magance musu matsalar jinnu.

Kaduna: Yarinya mai shekaru 12 da malami ya ɗirkawa fyaɗe ta haifi ɗa namiji

Wata yarinya ƴar shekara 12 a duniya wacce wani malamin makaranta yayi wa fyaɗe a unguwan Fantaro cikin ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna, a wajajen watan Yunin 2021, ta haifi ɗa namiji. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Malamin ya yaudare ta sannan yayi mata fyaɗe

Halima (ba sunanta na gaskiya ba) tana sayar da chin-chin, a ƙauyen su, lokacin da malamin mai suna Salihu ya yaudare ta cewa zai sayi chin-chin na N200.

Salihu ya rufe mata baki sannan yayi mata fyaɗe a cikin ɗakin.

Daily Trust ta samo cewa yarinyar ta ɗauki juna biyu watanni uku bayan aukuwar fyaɗen, inda aka miƙa ta a hannun ministirin jinƙai da walwala ta hannun gidauniyar Ummulkhairi Foundation.

An tabbatar da haihuwar yarinyar

Sai dai, yayin da ta ke tabbatar da haihuwar yarinyar, kwamishiniyar jinƙai da walwala ta jihar, Hajiya Hafsat Baba, ta bayyana cewa yarinyar ta haifi ɗa namiji cikin nasara.

Hajiya Hafsat Baba ta ce:

Ƙaramar yarinyar ta haifi ɗa namiji sati uku da su ka wuce, sannan ina farin ciki cewa likitoci a asibitin Barau Dikko sun bata kulawa ta haihu da kanta ba tare da an yi mata aiki ba.

Duk da dai jaririn yana hannun mu, mun miƙa ta zuwa wajen mahaifiyar ta ranar Laraba. Sai dai ba za mu yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin mun ƙwato mata haƙƙin ta a wurin wannan mutumin da ya jefa ta cikin wannan halin.

Ta yi nuni da cewa malamin yana garƙame a wurin hukuma tun lokacin da lamarin ya auku.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe