27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yadda aka siyar min da rubabbiyar doya a N2,500, har ana ce min mai inganci ce, wani mutum ya koka

LabaraiYadda aka siyar min da rubabbiyar doya a N2,500, har ana ce min mai inganci ce, wani mutum ya koka

A halin kunci da talaucin da jama’a su ke ciki, har yanzu wasu ba sa duba hakan su tausaya wa ‘yan uwansu bil Adama, LIB ta ruwaito.

Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter Uncle Sarm ya bayyana yadda aka damfare shi a Legas.

A cewarsa, ya ware kudi wuri na gugar wuri N2,500 don ya siya doyar da zai sa a bakin salatinsa amma ashe lalatacciya ce.

Kamar yadda ya wallafa hoton rubabbiyar doyar inda ya yi tsokaci ya ce:

“Ku taya ni ganin lalatacciyar doyar da aka siyar min N2,500. Na tsani Legas.

“Kuma mugun ce min ya yi wannan ce doyar da tafi ko wacce kyau ce.”

Yadda wani mutum ya yi yunkurin tserewa daga Najeriya bayan matarsa ta haifi yara 4 a lokaci guda

Wani dan Najeriya ya yi yunkurin guduwa jamhuriyar Benin bayan matarsa ta haifi yara 4 a lokaci daya.

Cissé Abdullahi mai shekaru 37, da matarsa suna sa ran haihuwar tagwaye bayan likitoci sun duba cikin yayin da ya girma.

Sai dai a ranar Litinin, 25 ga watan Afirilu matarsa ta haifi yara 4 a babban asibitin Badagry, LIB ta ruwaito.

Abdullahi, wanda ya ke tsaron shagon siyar da tayoyi ya tsere bayan samun labarin matarsa ta haifi yara 4 a lokaci guda.

Yayin da ya ke yunkurin guduwa ne abokinsa ya kwantar masa da hankali kuma ya tabbatar masa da cewa zai taimakeshi da kudin kulawa da yaran.

Duk da tallafin abokinsa, Abdullahi yana cikin mawuyacin yanayi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe