27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bayan Rarara ya gwangwaje shi da N50,000, yayan Ado Gwanja ya ce ba ya bukata, kaskanci ne

LabaraiKannywoodBayan Rarara ya gwangwaje shi da N50,000, yayan Ado Gwanja ya ce ba ya bukata, kaskanci ne

Yayan mawaki Ado Gwanja, Sa’idu Gwanja ya mayar da kyautar N50,000 da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi masa, inda ya ce ba ya bukata.

A wani bidiyonsa wanda Tashar Tsakar Gida ta wallafa, an ga inda Sa’idu ya ke bayyana hujjarsa ta kin amsar kudin.

yhayan gwanja
Bayan Rarara ya gwangwaje shi da N50,000, yayan Ado Gwanja ya ce ba ya bukata, kaskanci ne

Ya ce bai dace ace a tallatasu a kafafen sada zumunta ba, ana kiran sunayensu daya bayan daya, kowa yana ji ba, sannan a ba su kyautar N50,000.

Kamar yadda ya bayyana, yana da rufin asiri kuma akwai yaransa da marayun da ya ke kulawa da su, don haka Ubangiji ya rufa masa asiri.

A cewarsa, ta kan N50,000 ba za a kaskantar da shi ba a duniya. Ya ce ko a shekarar da ta gabata ma ya danne zuciyarsa ne shiyasa ya amsa bayan a lallashe shi. Amma a wannan shekarar ba ya so.

Ya yi fatan Ubangiji ya biya Rarara kuma ya ce ba ya yi masa hassada amma ba ya bukatar kudin saboda talaucinsa bai kai nan ba.

Ado Gwanja da tsohuwar matarsa, Maimunatu sun je Makkah yin Ummara, Allah ya daidaitasu

Yayin da mutane su ke ta tururuwar yin aikin Ummara a watan Ramadana, Labarun Hausa ta gano yadda mawaki Ado Gwanja da tsohuwar matarsa, Maimunatu suka tafi Saudiyya.

Sai dai alamu suna nuna cewa tafiyar kowa daban don yayin da suka sanya hotunansu a kafafen sada zumuntar zamani ta Instagram, kowa daban.

Tun a cikin jirgin sama Maimunatu ta fara daukar hotuna har lokacin da ta isa kasa mai tsarki.

Wannan kadai ya kara tabbatar da zargin mutuwar aurensu da mutane suka dinga yi kwanakin baya domin da suna da aure da tare za su tafi kuma su dauki hotuna tare.

Muna fatan Ubangiji ya daidaitasu ko kuma ya yi wa kowa zabi mafi alkhairi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe