24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Ke duniya: Uba ya ɗirkawa ‘yar cikin sa mai shekaru 15 ciki bayan yayi mata fyaɗe

LabaraiKe duniya: Uba ya ɗirkawa 'yar cikin sa mai shekaru 15 ciki bayan yayi mata fyaɗe

An cafke wani mutum mai shekaru 38 a duniya bisa laifin aikata fyaɗe ga ‘yar cikin sa mai shekaru 15 a duniya a jihar Ondo. Shafin LIB ya rahoto.

An cafke wanda ake zargin

‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargin, Sunday Udoh, bayan yayi yunƙurin zubar da cikin da yarinyar ta samu bayan ya sadu da ita.

Udoh ya kai ɗiyar ta sa zuwa wani asibiti a Ile-Oluji, domin a zubar da cikin.

Sai dai, jami’an kiwon lafiya a asibitin sun sanar da jami’an tsaro bayan sun fahimci akwai rashin gaskiya a tattare da shi.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ya bayyana cewa:

A ranar 26 ga watan Afrilun 2022, jami’an ‘yan sanda da ke a ofishin Ile-Oluji, sun amshi ƙorafin yunƙurin zubar da ciki da wani Sunday Udoh mai shekaru 38 yayi a wani asibitin a Ile-Oluji.

A yayin gudanar da bincike, an gano cewa wanda ake zargin yana yunƙurin zubar da cikin ɗiyar sa mai shekaru 15 wacce ya dinga saduwa da ita.

Kakakin hukumar ya kuma bayyana cewa zaa miƙa wanda ake zargin zuwa gaɓan kuliya bayan an kammala gudanar da bincike.

Kaduna: Yarinya mai shekaru 12 da malami ya ɗirkawa fyaɗe ta haifi ɗa namiji

Wata yarinya ƴar shekara 12 a duniya wacce wani malamin makaranta yayi wa fyaɗe a unguwan Fantaro cikin ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna, a wajajen watan Yunin 2021, ta haifi ɗa namiji. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Malamin ya yaudare ta sannan yayi mata fyaɗe

Halima (ba sunanta na gaskiya ba) tana sayar da chin-chin, a ƙauyen su, lokacin da malamin mai suna Salihu ya yaudare ta cewa zai sayi chin-chin na N200.

Salihu ya rufe mata baki sannan yayi mata fyaɗe a cikin ɗakin.

Daily Trust ta samo cewa yarinyar ta ɗauki juna biyu watanni uku bayan aukuwar fyaɗen, inda aka miƙa ta a hannun ministirin jinƙai da walwala ta hannun gidauniyar Ummulkhairi Foundation.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe