29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Jaruma Maryam KK ta yi wa wani malami Raddi, wanda ya ce Almajiri daya da allonsa ya fi gaba daya Kannywood daraja

LabaraiKannywoodJaruma Maryam KK ta yi wa wani malami Raddi, wanda ya ce Almajiri daya da allonsa ya fi gaba daya Kannywood daraja

Jarumar Kannywood mai tasowa, Maryam KK ta nuna rashin jin dadinta akan kalaman zargin fasikanci da wani malami yayi wa ‘yan kannwood.

A cewarta, ba ya da wata kwakkwarar hujjar da zai kare kansa akan zargin da yayi musu a ranar tashin qiyama, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito..

Jaruma Maryam KK ta yi wa wani malami Raddi, wanda ya ce Almajiri daya da allonsa ya fi gaba daya Kannywood daraja
Jaruma Maryam KK ta yi wa wani malami Raddi, wanda ya ce Almajiri daya da allonsa ya fi gaba daya Kannywood daraja

Jarumar ta fara da wallafa bidiyon a shafinta sannan ta yi tsokaci karkashin bidiyon tana cewa:

“Innalillahi wa inna ilayhi raji’un. Me ya hada almajiranci da Kannywood kuma? Babu wanda ya fi wani a wurin Allah sai wanda ya fi tsoronsa.

“Malam zaka iya shedar abinda ka fadi a ranar Lahira? Bara a musulunci haramun ne. Annabi SAW da kansa ya haramta yin bara.

“Wacce ake magana akanta bata zagi almajiranci ba. Kuma mun san darajar almajiranci. Shin a fin za ka ce babu nagari ko na banza?

“Da dana ya yi bara gara ya yi fim. Allah ka hana mu fadin abinda ranar lahira za a tashe mu bada shedar abinda muka fada ba mu da shi.

“Rayuwa kenan.”

Tashar Tsakar Gida ta haska wa’azin wanda malamin mai suna Sheikh Kasim Abdullahi Damagum ya yi inda ya ke cewa Almajiri daya da alonsa ya fi Kannywood daraja a wurin Allah.

Ya ci gaba da cewa babu abinda ke cikin Kannywood fae iskanci da fasikanci. Ya ce almajiranci gaskiya ne don akwai gwanayen Qur’ani a cikinsu.

Ya ce duk wanda ya taba almajirai, su ya taba don haka ba za su kyale shi ba sai sun fito sun yi masa kaca-kaca ba tare da wani abu ya same su ba.

Wasu na alakanta tallar maganin mata ‘kaca-kaca’ da Jaruma Umma Shehu ta yi da zargin lalatar matan Kannywood

Tun a makon da ya gabata rigima ke ta ruruwa a masana’antar Kannywood bayan mawaki kuma jarumi, Naziru Sarkin Waka ya zargi jarumai mata da bayar da kudi ko kuma jikin su don a haska su a fim.

Zargin ya yi matukar hassala su inda wasu suka fito suka yi masa wankin babban bargo suna cewa ya janye kalaman sa ko su maka shi a kotu.

Duk da dai a ranar Litinin an zauna a teburin sasanci da mawakin da hukumar tantance fina-finai tare da jiga-jigan masana’antar Kannywood inda aka sasanta su.

Sai dai, tsugunni bata kare ba, don wasu sun alakanta zargin da yake yi wa matan da wasu bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta na jaruma Umma Shehu.

Duk da dai jarumar bata da aure, amma an gan ta tana tallata magungunan mata na wata “Jarumar Mata” wacce ta yi fice a kafar Instagram.

Wani ma’aboci amfani da kafar Facebook kuma sananne, Datti Assalafy ya yi shimfida sannan ya wallafa bidiyon Umma Shehu tana tallata magunguna irin wadanda a cewarta mace ko ta gama lalata da maza zata koma tamkar budurwa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe