24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Wasu ‘yan Kannywood sun yi wa Sarkin Waka Dawafi suna fatan Allah ya yi musu sakayya akan kalamansa

LabaraiKannywoodWasu ‘yan Kannywood sun yi wa Sarkin Waka Dawafi suna fatan Allah ya yi musu sakayya akan kalamansa

Tsugunne bata kare ba dangane da rigimar Sarkin Waka da Nafisat Abdullahi, yayin da maganganu suke ta bullowa ko ta ina, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Wasu daga cikin ‘yan fim din sun goya masa baya yayin da wasu suka dinga caccakarsa musamman a Facebook da TikTok.

jaruman kannywood
Wasu ‘yan Kannywood sun yi wa Sarkin Waka Dawafi suna fatan Allah ya yi musu sakayya akan kalamansa

Yawancin wadanda suka je Saudiyya yin Ummara sun yi shiru ba tare da sun tofa komai ba ko kuma yin martani akan maganimun da ya yi.

Jarumi Malam Ibrahim Sharukhan, Suleiman Costome, mai haska dandali, Sani Candy da kuma Jarumi Adebo duk sun bayyana cewa sun yi dawafi inda suka kai kukansu ga Allah akan munanan maganganun da Sarkin Waka ya yi.

A cewarsu, sun yi dawafi inda suka kai karar Naziru wurin Allah akan ya yi musu sakayya da kuma maganganun da ya ke yi akan masana’antarsu.

Jarumi Malam Ibrahim Sharukhan ya fara da cewa:

“Da kai nake, wallahi a Makkah muke, garin ma’aiki muke, Allah ya kara wa Annabi daraja ya bar mu da soyayyarsa.

“Wallahi mun yi dawafi akanka kuma mun hada ka da Allah, kuma mun bar ka da shi. Allah ya yi mana sakayya.”

Daga nan Suleiman Costume ya ce:

“Ni babu abinda zan ce akanshi sai dai in ce mun bar shi da Allah.”

Ya ci gaba da cewa sana’arsu ita ce mutuncinsu don haka sun kai kara wurin Allah, Allah ya yi musu sakayya akan maganganun da ya yi akansu.

Tsugunne ba ta kare ba: Kungiyar matan Kannywood za su maka Nazir Sarkin Waka a gaban kotu kan kalaman da yayi

A daidai lokacin da wasu jaruman ke kokarin sanyawa lamarin wutar da ta tashi a masana’antar Kannywood ruwa, wasu kuwa kokari suke yi su kara tada wutar ta cinye kowa ma a huta.

A jiya ne dai Mawaki Nazir M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya sake yin wani sabon bidiyo, inda ya roki kowa yayi hakuri, ya kuma bayyana cewa duka maganganun da yayi ba wai yayi bane domin ya bata sana’ar wani ko sunan wani ba, kawai dai gaskiya ce ta fito kuma ya fade ta.

Tsugunne ba ta kare ba a Kannywood

Sai dai kuma alamu na nuni da cewa tsugunne bata kare ba a masana’antar, dominn kuwa kungiyar mata ta masana’antar Kannywood sun fitar da wata sabuwar takarda da suka bukaci Nazir ya janye kalaman sa.

Kungiyar ta bayyana cewa matukar Nazir bai janye kalamansa cikin kwanaki uku ba, to tabbas sai dai su hadu a kotu domin a bi musu hakkinsu kan cin zarafin su da yayi.

Abinda takardar ta bukaci Nazir ya yi

Takardar wacce kungiyar ta fitar a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022, ta yi bayani kamar haka:

“Assalamu Alaikum

Kungiyar mata ‘ta Kannywood Women Association Nigeria (K-WAN) karkashin jagorancin kungiyar, ni shugabar kungiya a madadin ‘yan kungiyar.

Duba da abin da ya faru, wanda Naziru M Ahmad ya yi wasu kalamai na cin zarafi ga mata masu sana’ar fim, muna kira gare shi da ya janye kalamansa cikin kwana uku daga yau, in kuwa bai yi haka ba za mu kai shi kotun Musulunci bisa tuhumar ya yi mana kazafi.


Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe