29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bidiyon Ummi Rahab da mahaifiyarta a Saudiyya suna rusa kuka bayan sun dade basu hadu ba

LabaraiKannywoodBidiyon Ummi Rahab da mahaifiyarta a Saudiyya suna rusa kuka bayan sun dade basu hadu ba

Wani bidiyo wanda Tashar Tsakar Gida ta sanya a shafinta na YouTube ya nuna yadda jaruma mai tasowa, Ummi Rahab, da mahaifiyarta suke ta rusa kuka.

Kamar yadda aka gansu, sun rungume juna tare da durkusawa kasa suna kukan wanda ya ja hankalin masu wucewa.

Bidiyon Ummi Rahab da mahaifiyarta a Saudiyya suna rusa kuka bayan sun dade basu hadu ba
Bidiyon Ummi Rahab da mahaifiyarta a Saudiyya suna rusa kuka bayan sun dade basu hadu ba

Tun bayan rikicin jarumar da tsohon ubangidanta, Adam A. Zango hotunan mahaifiyarta suka bayyana a yanar gizo.

Sai dai kamar yadda yayanta, Yasir ya nuna, mahaifiyarsu tana zaune ne a kasar Saudiyya kuma akwai lokacin da suka gana da ita da Adam Zango.

Haka zalika a ranar iyaye mata ta duniya, Mother’s Day, Jarumar ta wallafa wani guntun bidiyo a shafinta na Instagram inda ta hada hotunanta da na mahaifiyarta.

A wannan karon kuwa, ba hotuna bane, a fili ne suka hadu a kasar Saudiyya wanda suka dinga kuka mutane na ganinsu.

Dama jarumar ta je kasar ne don aiwatar da aikin Ummara wanda daga nan ta jefi tsuntsaye biyu da tarko daya.

Da dumin sa: Mawaki Lilin Baba yana shirye-shiryen auren jaruma Ummi Rahab

Fitaccen mawaki kuma jarumin shirin fim din Kannywood, Shu’aibu Ahmed Abbas, wanda kowa ya fi sani da Lilin Baba ya bayyana wa duniya cewa yanzu haka shirye-shiryen auren sa da jaruma Ummi Rahab ya kankama, Aminiya ta ruwaito.

Yayin tura sakon sa na yi wa jaruma Ummi Rahab fatan alheri a ranar da ta kara shekaru, ya tura sako gare ta kamar haka:

“Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki abar kauna ta, Ummi Rahab. Lallai kin kasance mutumiyar kirki ma’abociya zuciyar zinare.

“Ina tura miki sakon taya murnar zagayowar ranar da aka haife ki a daidai ranar da ki ka kara wata shekarar a rayuwar ki.

“Ina fatan yau za ta zama ranar murna a gare ki tare da farin ciki. Ina jin dadin ganin yadda kika samu ci gaba a rayuwar ki. Ina fatan Allah ya albarkaci rayuwar ki.”

Can a karshen wallafar tasa sai ya ce:

“Na kusa yin Wuf da ke in sha Allah!”

A karkashin wallafar, jarumar ta nuna jin dadin ta dangane da wallafar ta shi inda ta yi masa tsokaci.

Kamar yadda ta yi masa martani inda ta ce:

“Ina mika godiya ta abin kauna ta. Lallai kai ne a gaba cikin jerin mutane, mijina na nan gaba. Na kosa in ga ranar. Allah ya nuna mana.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe