27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yadda cingam ya yi ajalin wata mata bayan ga yi bacci da shi a bakinta

LabaraiYadda cingam ya yi ajalin wata mata bayan ga yi bacci da shi a bakinta

Wata mata, Sulwen Jones mai shekaru 55 ta rasa ranta yayin da ta kwanta bacci da cingam a bakinta, LIB ta ruwaito.

Dama tana amfani da cingam dinne kamar yadda likitoci suka bukaci ta yi don taimaka wa bakinta daga bushewa.

Sai dai an tsinci gawarta a gidanta da ke Caernarfon a North Wales.

cingam
Yadda cingam ya yi ajalin wata mata bayan ga yi bacci da shi a bakinta

‘Yar uwarta ta tsinceta a mawuyacin yanayi a ranar 5 ga watan Oktoban 2021 amma ba a gano silar hakan va.

A wannan makon, The Inquest ta gano yadda matar ta sha maganin cutar multiple sclerosis wanda ta kwashe shekaru 20 tana fama da cutar kafin mutuwarta.

Tana fama da wata cuta

Sulwen tana yawan cin cingam saboda bushewar makoshinta.

Parametrics ta bayyana yadda ake zargin matar ta rasu ne yayin da ta yi bacci da cingam wanda ya shaketa har lahira.

Yayin da aka tsananta bincike ne aka gano cingam din ya bi gaba daya jikinta har inda iska ya kamata ta bi wanda ya yi ajalinta.

Sojoji sun yi harbi a kasuwa wanda ya yi ajalin ‘yan mata guda biyu a Jihar Kaduna

Wasu ‘yan mata guda biyu sun rasa rayukansu sanadiyyar harsasan da sojoji suka harba a kasuwan gundumar Kidandan, wata anguwa karkashin karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda ganau suka bayyana, sojojin sun tuko motarsu ta cikin kasuwa, yayin da suka hango wasu mutane zaune akan barubura, hakan yasa suka fara yi musu tambayoyi.

Mazauna kauyen sun ranta a na kare, a lokacin da suka fara jin karar harbin bindigar da ake zargin sojojin ne suka bude wa wadannan mutanen wuta.

Yayin luguden wutar, ‘yan mata guda biyu, Nuratu, mai shekaru 16 da Khadija, mai shekaru 11, sun samu harbin harsasan a lokacin da suka yi kokarin tserewa daga wurin.

Babban yayan su, Salisu Shuaibu Kidandan, ya bayyana wa Daily Trust yadda yaran suka rasa rayukansu sanadiyyar harsasan da sojojin suka harba a cikin jama’a.

“Duk da sun yi ( sojojin) nufin harbin Fulanin da suka gani a kasuwar, don me zai sa su harba cikin taron mutane?

“Yan uwa na sun yi kokarin tserewa zuwa gida, saboda kasuwa na wajen garin kauyen, yayin da aka bude musu wuta,” a cewarsa.

A halin yanzu da muke magana, sojojin basu zo yi wa iyayenmu ta’aziyya akan abunda suka aikata ba, ‘yan sanda ne kadai suka yi hakan.

“Muna bukatar a yi mana adalci, saboda baza a halaka salahan yara haka kawai a tafi ba,” a cewarsa.

Haka zalika, wani mazaunin kauyen ya ce, bai kamata ace sojojin sun yi harbin a kasuwa ba, saboda Fulanin sun yi nufin tserewa cikin daji ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe