26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda wani mutum ya yi yunkurin tserewa daga Najeriya bayan matarsa ta haifi yara 4 a lokaci guda

LabaraiYadda wani mutum ya yi yunkurin tserewa daga Najeriya bayan matarsa ta haifi yara 4 a lokaci guda

Wani da Najeriya ya yi yunkurin guduwa jamhuriyar Benin bayan matarsa ta haifi yara 4 a lokaci daya.

Cissé Abdullahi mai shekaru 37, da matarsa suna sa ran haihuwar tagwaye bayan likitoci sun duba cikin yayin da ya girma.

tserewa
Yadda wani mutum ya yi yunkurin tserewa daga Najeriya bayan matarsa ta haifi yara 4 a lokaci guda

Sai dai a ranar Litinin, 25 ga watan Afirilu matarsa ta haifi yara 4 a babban asibitin Badagry, LIB ta ruwaito.

Abdullahi, wanda ya ke tsaron shagon siyar da tayoyi ya tsere bayan samun labarin matarsa ta haifi yara 4 a lokaci guda.

Yayin da ya ke yunkurin guduwa ne abokinsa ya kwantar masa da hankali kuma ya tabbatar masa da cewa zai taimakeshi da kudin kulawa da yaran.

Duk da tallafin abokinsa, Abdullahi yana cikin mawuyacin yanayi.

Sabon ma’aikacin gidan burodi ya sace N350,000, ya tsere a jihar Legas

Wani ma’aikacin gidan burodin Tasty Loaf Bakery dake titin Ajelogo lamba 12 a unguwar Mile ta jihar Lagos, mai suna
John Emeka, ya sace Naira 350,000
mallakar gidan burodin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, anga wanda ake zargin a cikin talabijin sirri ta gidan burodin, yayin da yake tserewa da kudin, wanda aka ce cinikin ranar Larabar 16 ga watan Maris ne gabaki daya.

An nemi Emeka din ne, wanda shine mai siyadda burodin, an rasa da shi da kudin tun kafin lokacin tashi.

Kamfanin burodin ya kai rahoton lamarin ga ofishin yan sanda na Mile mai lamba 12.

Wakilin jaridar Punch yace, wanda ake zargin ya bar wayarsa a kamfanin bayan ya cire layin ta, inda ya gudu zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kamar yadda diddigin layinsa ya nuna.

A fadar mai kamfanin Motunrayo Odusi, mai laifin ya gudu da kudin ne da misalin karfe 5:48pm na yamma, kamar yadda na’urar CCTV ta bayyana.

Tace : ” Mijina ne ya hadu da Emeka a gidan sayadda abinci, inda yayi aiki, sai ya gabatar wa da mijina wani abokin sa Victor, kuma ya roki mijina akan yana so ayi masa alfarma Victor din yayi aiki da mu.

” Bayan wata daya sai ya sake kiran mijina a waya, yace masa ya rasa aikin sa na gidan abinci, yana rokon da mu daukeshi aiki, inda muka yarda muka daukeshi.

“Bayan sati biyu da daukar sa ya sake rokon alfarma cewa yana so ya zauna a gidan mu na kamfani saboda yana da matsalar gurin zama, muka yarda ya zauna.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe