24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Matar wani babban basaraken Yarbawa ta musulunta

LabaraiMatar wani babban basaraken Yarbawa ta musulunta

Olori Joyce Anene Balogun, matar Olubadan ɗin Ibadanland, Oba Lekan Mohood Balogun, ta ƙarbi addinin musulunci. Shafin LIB ya rahoto

Matar basaraken ta shiga addinin musulunci cikin watan Ramadan

Olori Joyce Anene Balogun ta ƙarbi addinin musulunci a lokacin wata lakcar watan Ramadan wacce aka gudanar a ranar Litinin 25 ga watan Afrilu, a babban filin masallacin idi na birnin Ibadan ƙarƙashin jagorancin honorabul Ibraheem Akintayo. 

626924f9d44ab
Matar wani babban basaraken Yarbawa ta musulunta. Hoto daga LIB

An tabbatar da shigar ta musulunci

Babban limamin jihar Oyo, Sheikh Abdul Ganiyy Abubakry Agbotomokekere I, ya tabbatar da labarin a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook, inda ya ƙara da cewa sabon sunan sarauniyar na yanzu shine Khadijah Mahood Lekan Balogun. 

Olori Joyce Mahood Lekan Balogun {Olori Olubadan ɗin Ibadanland} ta ƙarbi addinin musulunci a hannun babban limamin jihar Oyo mai girma Sheikh Abdul Ganiyy Abubakry Agbotomokekere a ƙaramar hukumar Ibadan ta Arewa yayin gudanar da lakcar watan Ramadan a babban masallacin Idi na Ibadan {Yidi Agodi Gate Ibadan} a ƙarƙashin jagorancin honorabul Ibraheem Akintayo {Sunan Olori na yanzu Khadijah Mahood Lekan Balogun.

A cewar sanarwar

Muhimman abubuwa 8 da yakamata ku sani dangane da marigayi Oba Adeyemi, Alaafin na Oyo

Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya rasu a daren ranar Juma’ah, wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkin sa na tsawon shekaru 52 a akan sarautar.

Mai shekaru 83 a duniya, Oba Adeyemi, wanda ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola, a birnin Ado Ekiti na jihar Ekiti, shine Alaafin na Oyo wanda yafi daɗewa akan karagar mulki.

Abubuwan sani dangane da Oba Adeyemi

A yayin da ake jiran shirye-shiryen binne basaraken, jaridar Daily Trust ta tattaro wasu abubuwa 8 waɗanda su kayi duba akan rayuwar Oba Adeyemi

1. Haihuwar sa

An haifi Oba Adeyemi a 15 ga watan Octoban 1938, a gidan sarautar Alowolodu, ya fito daga tsatson gidan Oranmiyan. Mahaifiyar sa Ibironke, ta rasu lokacin yana ƙarami. Mahaifin sa marigayi Adeniran Adeyemi, ya zama Alaafin a shekarar 1945.

2. Ya hau sarauta yana matashi

Oba Lamidi Adeyemi III ya hau karagar Alaafin a shekarar 1970 lokacin yana da shekaru 31 a duniya a ƙarshen yaƙin basasa na Najeriya. Ya zaman sarki ne a lokacin da  Colonel Robert Adeyinka Adebayo yake gwamnan soji na jihar Oyo.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe