27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Gadararre, Mai Girman Kai, Tun da ta bar fim dinka ka dauki tsana ka daura mata, Martanin Baban Chinedu ga Sarkin Waka

LabaraiKannywoodGadararre, Mai Girman Kai, Tun da ta bar fim dinka ka dauki tsana ka daura mata, Martanin Baban Chinedu ga Sarkin Waka

Yayin da rigimar Naziru Sarkin Waka da Jaruma Nafisat Abdullahi ta ke kara nisa, jarumai suna ta mata mata baya yayin da wasu suke goyon bayansa.

Tsohon jarumi kuma mawaki, Baban Chinedu ya fito fili ya fallasa Naziru Sarkin dalilin da yasa Naziru da Jaruma Nafisat Abdullahi suka samu sabani.

bbn chinedu
Gadararre, Mai Girman Kai, Tun da ta bar fim dinka ka dauki tsana ka daura mata, Martanin Baban Chinedu ga Sarkin Waka

A cewarsa, hakan yana da alaka da yadda ta zame jiki daga fim dinsa, Labarina mai farin jini. Kuma cutarta suka yi, kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo da Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Ya bayyana dalilin rashin jituwar Naziru da Nafisat

Baban Chinedu ya bayyana yadda Naziru ya amshi miliyoyin Nairori daga hannun gwamnati don tallatata a shirinsa, amma bai dauki ko sisi ya ba jaruman ba face kudin aikinsu.

A cewarsa, ganin ya dena tallar kuma kudi ya tsaya da shigar masa yasa ya tsani Nafisat Abdullahi kasancewar ita ce jarumar da ta haska fim din.

Baban Chinedu ya kira Naziru da mai girman kai, takama da gadara, inda ya ce yana yawan samun matsala da makwabtansa saboda bakin halinsa.

A cewarsa, in har Naziru ya ci gaba da amfani da matsalarsu da Nafisat Abdullahi yana maganganu, sai sun fallasa shi a idon duniya.

A dogon bidiyon da mawakin ya yi ya ce Naziru yana da kyamar Almajirai amma saboda matsalar da ke tsakaninsa da Nafisat Abdullahi ya sa ya sauya mata maganganu.

Yayin da ya ke bayanin, ya ce Naziru abokinsa ne, ita kuma Nafisat ko lambarta ba ya da ita, saboda ba ta cikin wadanda suke shiri a masana’antar amma idan maganar gaskiya ta zo a yita.

Martanin Nafisa Abdullahi ga Sarkin Waka: Na san matsalarka, so kake kayi suna

Shahararriyar jarumar masana’antar fina-finai ta Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kakkausan raddi ga Naziru Ahmad wato Sarkin waka.

Nafisa Abdullahi ta caccaki Sarkin Waka

A wata wallafa da jaruma Nafisa Abdullahi tayi a shafin ta na Twitter, jarumar ta caccaki Naziru Ahmad inda ta bayyana shi a matsayin mai neman suna.

Tun da farko dai Naziru Ahmad yayi wata wallafa a kafar sadarwa wacce ta ke a matsayin raddi akan maganar da Nafisa Abdullahi tayi akan matsalar almajirai a ƙasar Hausa.

Mutane sun bayyana ra’ayoyin su

Raddin da jarumar ta yi ya sanya mutane da yawa sun tofa albarkacin bakin su. LabarunHausa ta tattaro ma ku wasu daga ciki.

@abdulahmed332 ya rubuta:

Kodai kin hana shu kaya ne shine abunda ke bothering din sa

@Gamasadic ya rubuta:

Mai kashi a gindi baya surutu da yawa Yana da abun fada amma in ba hanyar fada masa shuru ake ana  kallonsa da abun amma fa da zarar yabada kofa tofa Sai abun da ya gani Allah yasa mudace.


Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe