23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An sha mu mun warke: Matasa sun yi caa akan dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba II, bayan ya ce a tara masa kudin fom

LabaraiAn sha mu mun warke: Matasa sun yi caa akan dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba II, bayan ya ce a tara masa kudin fom

Fitaccen dan gwagwarmaya kuma matashin dan takarar shugaban kasar nan, Adamu Garba II ya sha caccaka bayan ya bukaci a tara masa kudin fom din takarar shugaban kasa.

Ya kara wallafa wata wallafa ranar Asabar wace shafukan kafafen sada zumuntar zamani na Arewa Reporters da KBC Hausa News suka yi.

adamu11
An sha mu mun warke: Matasa sun yi caa akan dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba II, bayan ya ce a tara masa kudin fom

Wallafar tana nuna bukatarsa ta kudade daga jama’an Najeriya don ya samu ya siya fom din takarar shugaban kasa musamman ganin shi matashi ne.

A wallafar, akwai asusun bakinsa wanda a wata wallafa ta daban da ya yi a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa ya samu N2m daga jama’a maso mara masa baya, kuma har yanzu ana ci gaba da tura masa.

Sai dai, LabarunHausa.com ta lallaba karkashin wallafar morning ta shi don jin tsokacin jama’an wanda da dama suke nuna cewa wani salon yaudara ne ya fara kamar yadda ‘yan siyasar baya suka yi.

Wani Umar Ahmed Ibrahim ya ce:

“Ga wani salo na yaudara. Ba za a yaudare mu har sau biyu ba.”

Muhammad Zayyan ya ce:

“Dan Allah in an hada mishi kudin ya bani ko quarter ne daga cikin su Adamu Garba II.”

Ibrahim Datti ya ce:

“Canji ya ragee a wancan damuka sayawa Shugaba Mai ci yanzu.”

Abubakar Suleiman ya ce:

“Wani sabon dan hanyar ne kenan, haba guy munga Buhari ma Alaji.”

Sheikh Hamisu A. Walih ya yi tsokaci da:

“Ba za mu tura ba, baya ma mun yi mun ga abinda muka gani.”

Ameen Mahmoud Aleeyou ya ce:

“Alaji ai ansha mu mun warke akan Buhari, babu mugun da zamu kara hadawa ‘yan canjin mu.”

Comr Over over ya ce:

“Gaibu kenan.”

Umar Sadi ya ce:

“Wai dama duk cika bakin da kakeyi bakada 100m?

Ai ni ko zaben ma bazan yi ba ballantana na tura kudi ka siya form.”

Matasa Bismillah: APC ta tsayar da N100m a matsayin kudin takarar shugaban kasa, N50m na gwamna

Jam’iyyar APC tsayar da N100 miliyan a matsayin kudin fom din takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 da ke kara matsowa, LIB ta ruwaito.

An tsayar da kudin ne ne yayin taron gaggawar na kwamitin zartarwar jam’iyyar, NEC wanda tayi a Abuja, yau 20 ga watan Afirilu.

Jam’iyyar ta sanar da kudin fom din takarar gwamna a N50 miliyan, majalisar dattawa N20 miliyan da majalisar wakilai N10 miliyan.

Inda jam’iyyar ta sanar da fara sayar da fom din takar a ranar Asabar, 23 ga watan Afirilu.

Yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron, sakataran watsa labarai na kasa, Felix Morka, ya ce kudin siyan fom din takarar shugaban kasa zai kama N70 miliyan, yayin da N30 miliyan zai zama na bayyana ra’ayi a Jam’iyyar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe