24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda wasu matasa suka tasa wa barawo taliya, bayan ya lamushe suka hau jibgarsa

LabaraiYadda wasu matasa suka tasa wa barawo taliya, bayan ya lamushe suka hau jibgarsa

An ba wa wani da ake zargin barawon kebur ne kwanon taliya, yayin da ake mishi horo a yankin Agorogbene na karamar hukumar Sagbama dake jihar Bayelsa, LIB ta ruwaito.

An kama wanda ake zargin, Preye Ayase da abokin harkarsa, Ringo Tareladei dumu-dumu suna satar keburan wutar da ke sada Ogobiri da yankin Agorogbene cikin Sagbama a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu.

taliya
Yadda wasu matasa suka tasa wa barawo taliya, bayan ya lamushe suka hau jibgarsa

Sai dai, Oiseibai Seperegha Godsgift M, shugaban kungiyar matasan yankin (CYA) ya yi alawadai da barnatawa, sacewa gami da tarwatsa wayoyin wutan da ke sada yankunan biyu da hatsabiban suka yi.

A wata takarda da babban sakataran watsa labaran shi, Mr Ebis Okpeke ya bayyana wa manema labarai, na nuna yadda shugaban kungiyar ya nuna rashin jindadinsa bisa aukuwar lamarin ba tare da zato ba, inda ya yi kira ga matasan yankin da su bar irin wannan mummunar dabi’ar, saboda hakan zai zama sanadiyyar lalacewar rayuwarsu, ta hanyar kawo cikas ga cigabansu.

Kamar yadda takardar ta zo, shugaban ya ce:

“Da matukar takaici a ce an kama matasa suna lalata mana wutar lantarkinmu, wacce da kadan ta dara babu da sunan neman kudi.

“Abun karin takaicin shi ne musamman yanzu da mu ke fafutukar ganin wutar lantarkinmu ta fi haka, duba da yadda aka nuna halin ko in kula na tsawon shekaru.

“A nawa ra’ayin, ina jin radadi a ce matasan da ya kamata su kula mana da kayayyakinmu su ne ke assasa irin wadan nan munanan dabi’un.”

Ya ci gaba da cewa:

“A saboda haka ne, na ke bukatar wadanda ke da mummunan tunani irin wannan da su dena, sannan su nemi wata sana’ar da zata amfani al’umma ko kuma su shirye fuskantar cikakken fushin shari’a idan aka kamasu.”

Daga karshe, shugaban CYA ya yi amfani da damar wajen kira ga gwamnatin jihar Bayelsa da ta kawo wa yankunan da hakan ya shafa dauki don gyara wutar lantarkin Agorogbene, inda ya ce wutar lantarki na da matukar mahimmanci wajen bunkasa kananan masana’antu a yankin.

Bidiyo: Yadda barawon da sace kaji 3 ya boyesu da ransu cikin wandonsa

An yi ram da wani barawon kaji wanda ya rasa inda zai boye su sai cikin wandonsa, LIB ta ruwaito.

Wani mutum dan kasar Ghana ya yi yunkurin boye kajin da ya sace a cikin wandonsa, daga bisani ya sanya wandon don kada a gane shi.

Sai dai buyar bata yuwu ba bayan mutane sun farga inda suka kama shi da kajin dumu-dumu.

Mazauna yankin sun kama shi sannan suka cire kajin daga wandon nasa yayin da suka dinga yi masa bidiyo.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe