27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Matashiya ta siye kayan dattijuwa mai gyangyadi da kudin da yafi jarinta, tace ta je gida ta yi bacci

LabaraiMatashiya ta siye kayan dattijuwa mai gyangyadi da kudin da yafi jarinta, tace ta je gida ta yi bacci

Wata matashiya ta yi amfani da kudinta ta baiwa wata dattijuwa da ta kula tana gyangyadi a wurin karamar sana’ar ta, taimako.

Matashiyar ta baiwa dattijuwar wasu kudi da suka zarce kimar abin da take siyarwa.

Gyangyadi
Wata matashiya ta yi amfani da kudinta ta baiwa wata dattijuwa da ta kula tana gyangyadi a wurin karamar sana’ar ta, taimako.
Matashiyar ta baiwa dattijuwar wasu kudi da suka zarce kimar abin da take siyarwa.

Yan Nageriya da yawa sun yabawa matashiyar, inda da yawa suke cewa dattijuwar fa ba Lallai ta tafi gidan ba, kamar yadda aka ce mata.

Wata matashiya yar Najeriya, a wani shafin instagram mai suna @jojooflele, da aka yada, ta sanya farin ciki ga wata dattijuwa, inda a sakamakon haka akayi ta yaba mata.

A bidiyon da aka yada, matashiyar taga dattijuwar ne ta gaji, inda take ta gyangyadi agaban kayan da take siyarwa a kasuwa.

Mama tafi gida kiyi bacci

Ta tafi kai tsaye, ta tashi dattijuwar. Bayan ta tambaye ta nawa ne gaba dayan abin da take siyarwa, sai kawai ta biya duka, tace dattijuwar ta tafi gida tayi bacci.

Dattijuwar ta kasa zama dan murna, inda ta rungume matashiyar, kana ta surkusa har kasa tana godiya.

Lokacin da @yabaleftonline, suka sake yada bidiyon, ya sami sama da yabo dubu 16,000, a lokacin da ake hada wannan rahoton.

Ga wasu daga cikin sharhin da aka tattara.

spunkysessentials yace : “Idan dai har baki, kwace kudin ba, bayan an gama bidiyon, to Allah ya maki albarka “

itskokopee yace : “Bari in tabbatar miki da cewa bazata tafi gidan ba, mu yan Najeriya bazamu huta ba, dadin wahala muke ji”

johnpeshy yace : “Bazata taba mantawa da wannan ranar ba, Oh Nima Allah na roke ka kasa ina taimaka wa wasu”

iam.sharonjay yace : ” Tabbas Nima ina so inga na sanya wa wani farin ciki”

churchill_777 yace : “Bazata tafi gidan nan ba fa, sai ta tsaya ta siyadda komai tukunna, iyayen nan namu? Hmm.”

officalujunwa yace : “Wannan yayi kyau, amma na tabbata Mama fa bazata tafi gidan nan ba.”

Makwabci ya shiga har gida ya halaka matar aure da ɗiyarta da adda a jihar Kebbi

An cafke wani ɗan ƙasar Nijar bisa halaka wata matar aure da ɗiyarta mai shekaru 4 a jihar Kebbi.

LIB ta ruwaito cewa matar mai suna Sadiya Idris mai shekaru 25 tare da ɗiyarta Khadija, an samu gawarwakin su a gidan su da ke a titin Labana kan kwanar Sani Abacha, a Birnin Kebbi ranar 11 ga watan Afrilu.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, yayin tasa ƙeyar wanda ake zargin a hedikwatar hukumar a  Birnin Kebbi ranar Laraba 20 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa wanda ake zargin amsa aikata laifin.

Ya halaka matar auren da adda

A ranar 11/04/2022 da misalin ƙarfe biyu na dare, wani mai suna Idris Suleiman mai shekaru 25 a duniya daga Maradi, cikin Nijar, ya shiga gidan wani Akilu Aliyu, mazaunin titin Labana, akan kwanar Sani Abacha a Birnin Kebbi, inda yayi amfani da adda ya halaka matarsa mai suna Sadiya Idris mai shekaru 25 tare da ɗiyarta mai suna Khadija Akilu mai shekaru 4 a duniya.

Bayan samun rahoton, jami’an dake a sashin kula da kisan kai, (SCID) sun gudanar da bincike inda su ka samu nasarar cafke wanda ake zargin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe