24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Turawa sun rike wuta: Yadda wata baturiya ta garzayo Najeriya don auren wani matashi da suka hadu a Facebook

LabaraiTurawa sun rike wuta: Yadda wata baturiya ta garzayo Najeriya don auren wani matashi da suka hadu a Facebook
  • Bright Cletus Essien, ya angwance da masoyiyarsa baturiya, Jaclynn Annette Hunt, wacce ta hadu da Bright a Facebook, sannan ta garzayo Najeriya don halartar taron farinciki, wanda babu daya daga cikin mutanenta da yazo
  • Wani abokin angon wanda ya wallafa katin gayyatar a Facebook ya bayyana yadda masoyan suka fara soyayya daga hira a kafar sada zumunta

Wata Injiniya ‘yar kasar Amurka mai suna Jaclynn Annette Hunt tayi wuff da wani ‘dan Najeriya, Bright Cletus Essien, Legit.ng ta ruwaito.

Baturiyar ta niko gari zuwa Najeriya don halartar bikin aurenta da masoyinta, wanda ya gabata a ranar Lahadi, 17 ga watan Afirilu a Cocin Divine Dominion Covenant na Obio Ibiono dake Akwa Ibom.

baturiya da ango
Turawa sun rike wuta: Yadda wata baturiya ta garzayo Najeriya don auren wani matashi da suka hadu a Facebook

Sai dai abun mamakin shi ne yadda babu daya daga cikin dangin tsaleliyar amaryar ‘yar birnin Detroit da ya halarci taron da ‘yan uwa da abokan arzikin angon suka cika wurin.

Wani abokin angon, Alban Ekandem yayin bada sanarwa a Facebook ya bayyana yadda masoyan suka hadu a kafar sada zumuntar zamanin.

Alban ya kara da cewa, da farko ya yi zaton karya ne a lokacin da aka gayyaceshi bikin.

Ya taya abokinshi, angon murna akan yadda ya nuna mishi kurensa, gami da nuna cewa babu abunda so bai zai iya janyowa ba.

Ga abunda ya rubuta:

“A lokacin da ya gayyace ni bikin, ce mishi nayi kai karya ne, ya yi murmushi, sannan ya ce dan uwa tana nan zuwa, daga karshe dai ga ta nan tare damu.

“Soyayyar ta fara ne a Facebook da gaisuwa, sannan ta amince da aurensa.

“Daga karshe dai Bright ka tabbatar min da cewa babu abunda ya gagari so. Muna yi wa Jaclyn barka da zuwa Akwa Ibom, Najeriya.

“Gobe ne ranar. Daren gauro ya kusa farawa. Za ku iya zuwa wurin mu da dare.

“Ina maka murna ‘dan uwa. Naji muku dadi matuka.”

Haka zalika, Alban ya wallafa hotunan shagalin bikin ma’auratan, wanda ya janyo tsokaci daga ‘yan Najeriya da dama.

Ga wasu daga ciki.

Inyang ya ce: “Amma bari in tambaya.

“Meyasa aka yi shagalin bikin a Ibiono?

“Bai kamata ace an yi a garin amaryar bane?

Mike Ebong ya ce:

“Lallai an kafa tarihi a Obio ital, inda baturiya tazo auren wani mutum. Ina tayaka murna ‘dan uwa, mu kakarmu ta yanke saka.”

Samuel Isang ya ce:

“Ina mishi murna, amma fa mata da mazan Detroit suna da babban hatsari ko a Amurka. Ya dai bi a hankali.”

Ikoedem Johnson ta ce:

“Ina taya su murna, amma ku fada mishi ya yi saurin daukar baturiyar nan zuwa sashin rigistar aure kafin ta tsere, hakan na da matukar mahimmanci fa.”

Baturiyar da ta halaka saurayinta dan Najeriya a kasarsu ta ci gaba da walwalarta, har da zuwa mashaya

An ga wata baturiya da ta halaka saurayinta dan Najeriya ta hanyar daba masa makami a mashaya tana shan giya tare da mahaifinta, yayin da dangin wanda ta halakan suke zaman makoki, LIB ta ruwaito.

Courtney Tailor Clenney ta halaka Christian Toby Obumseli, dan Najeriya sannan mazaunin Amurka ta hanyar daba masa wuka a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu, a mazauninsu dake Miami.

Anyi ram da Courtney, amma sai tayi barazanar halaka kanta, hakan yasa ‘yan sanda suka mikata ga asibitin mahaukata karkashin dokar Baker.

A Florida, jami’an tsaro na da damar mika mutum asibitin mahaukata na tsawon kwanaki uku ta hanyar amfani da dokar kasa ta Baker.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe