23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Hukuma ta yi ram Amaryar da ta hada kai da mai girkin bikinta wurin zuba kayan maye a abinci, jama’a suka dinga marisa

LabaraiHukuma ta yi ram Amaryar da ta hada kai da mai girkin bikinta wurin zuba kayan maye a abinci, jama’a suka dinga marisa

Hukuma ta kama wata amarya da mai girkin bikin da ake zargin sun hada kai wurin zuba kayan maye a cikin abincin biki, LIB ta ruwaito.

Ana zargin amaryar, Danya Shea Glenny Svoboda mai shekaru 42 da mai girkin bikinta, Jocelyn Montrinice Bryant mai shekaru 31 sun zuba wiwi a cikin abincin baki bisa mugunta.

WhatsApp Image 2022 04 22 at 12.38.29
Hukuma ta yi ram Amaryar da ta hada kai da mai girkin bikinta wurin zuba kayan maye a abinci, jama’a suka dinga marisa

Bikin wanda aka yi a The Springs Clubhouse da ke Longwood a Florida a ranar 19 ga watan Fabrairu, ya samu halartar baki 50.

Sai dai bakin sun dinga marisa bayan sun ci abinci iri-iri da ke dauke da tabar wiwi.

Yayin da aka tambayi angon, Andrew Svoboda, idan na shi bakin sun san abinda ya ke cikin abincin, cewa ya yi a’a.

amaryar da angonta
Amaryar da angonta

Daga bisani aka dinga gwaje-gwaje na kwanuka da kofinan da aka yi amfani da su, inda aka gano suna dauke da kayan maye.

Wata mata ta kada baki ta cewa ‘yan sanda:

“Na ji kai na ya kulle, na rasa inda zan sa kaina yayin da zuciyata ta fara min sake-sake sannan kwakwalwata ta dinga juyawa.

“Sai na ji kamar sirikina ya rasu amma ba a sanar da ni ba.”

‘Yan sanda sun ruwaito yadda bakin duka dinga yin marisa har sai da aka samo musu magani daga asibiti.

Wata bakuwar da ta halarci bikin cewa ta yi ta dinga yin tunani iri-iri yayin da zuciyarta ta dinga bugawa da sauri.

Wata kuma cewa ta yi amai ne ya zo mata sannan ta ji kasala ta lullubeta, hakan ya sa ta nemi mota ta mayar da ita gida.

Bayan kammala duk gwaje-gwajen asibiti, an gano alamun kayan maye yayin da duk bakin basu san abinda suka ci ba.

Bayan tsare amaryar da mai girkin, an sake su yayin da za su gurfana gaban kotu a ranar 7 ga watan Yuni.

Zan halaka rai 300 idan ba a biya ni N30m ba na fansar ran amaryata ba, Ɗan bindiga ya ba Matawalle kwana 14

Dan bindiga Nasanda ya baiwa gwamnatin jihar Zamfara wa’adi da ta biya miliyan 30 nan take

Dan bindiga yana bukatar kudin ne, saboda zargin kisan wasu yan aikin sa ido, suka yi wada amaryar sa da kuma wasu yan uwansa.

A fadar dan bindigan, zai kashe mutum 300, idan ba’a yi abin da ya nema ba.

A wani sako da ya girgiza yan Nageriya, wani dan bindiga da ake kira da Nasanda, ya fitar da wani wa’adi ga gwamnatin jihar Zamfara da ta biya shi Naira miliyan 30.

Yace za’a biya shi kudin ne a matsayin fansa ga kisan da aka yi wa matarsa da kuma wasu yan uwansa guda biyu.

Dan bindigan ya ce, idan ba’a biya shi wannan kudin ba, to zai kashe mutum 300, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Nasandan yayi ikirarin cewa, ‘yan bijilanti ne suka kashe amaryar sa, kawunta da matar kawunta.

A rahoton jaridar, ance ya fitar da sakon ne ta hanyar nadar sakon murya.

Nasanda din yace, yan bijilantin wadanda suka kashe amaryar tasa, da yan uwanta, su kashe sune da gayya, domin sun san su suna da alaka dashi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe