23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Makwabci ya shiga har gida ya halaka matar aure da ɗiyarta da adda a jihar Kebbi

LabaraiMakwabci ya shiga har gida ya halaka matar aure da ɗiyarta da adda a jihar Kebbi

An cafke wani ɗan ƙasar Nijar bisa halaka wata matar aure da ɗiyarta mai shekaru 4 a jihar Kebbi.

LIB ta ruwaito cewa matar mai suna Sadiya Idris mai shekaru 25 tare da ɗiyarta Khadija, an samu gawarwakin su a gidan su da ke a titin Labana kan kwanar Sani Abacha, a Birnin Kebbi ranar 11 ga watan Afrilu.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, yayin tasa ƙeyar wanda ake zargin a hedikwatar hukumar a  Birnin Kebbi ranar Laraba 20 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa wanda ake zargin amsa aikata laifin.

Ya halaka matar auren da adda

A ranar 11/04/2022 da misalin ƙarfe biyu na dare, wani mai suna Idris Suleiman mai shekaru 25 a duniya daga Maradi, cikin Nijar, ya shiga gidan wani Akilu Aliyu, mazaunin titin Labana, akan kwanar Sani Abacha a Birnin Kebbi, inda yayi amfani da adda ya halaka matarsa mai suna Sadiya Idris mai shekaru 25 tare da ɗiyarta mai suna Khadija Akilu mai shekaru 4 a duniya.

Bayan samun rahoton, jami’an dake a sashin kula da kisan kai, (SCID) sun gudanar da bincike inda su ka samu nasarar cafke wanda ake zargin.

6260715a74272
Wanda ake zargi Idris Suleiman. Hoto daga LIB

Wanda ake zargin ya amsa laifin sa

A yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya tabbatar da halaka matar saboda ta kira shi da sunan dabba yayin da gardama ta ɓarke a tsakanin su.

Ya kuma ƙara da cewa ya halaka ɗiyarta mai shekaru 4 a duniya saboda yarinyar ta gane shi. Ana cigaba da gudanar da bincike sannan zaa tura wanda ake zargin gaban kotu da zarar an kammala gudanar da bincike. A cewar sa

Kano: ‘Yan sanda sun cafke wasu ƙananan yara bisa halaka wata matar aure saboda wayar salula

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wani yaro mai shekaru 18, Abdulsamad Suleiman, wanda ke zaune a Dorayi Chiranchi Quarters, Gwale, cikin birnin Kano, tare da abokin harƙallar sa Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, bisa zargin hallaka wata matar aure. Jaridar Punch ta rahoto

Kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar SP Abdullahi Haruna, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis ya bayyana cewa:

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe