28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Matasa Bismillah: APC ta tsayar da N100m a matsayin kudin takarar shugaban kasa, N50m na gwamna

LabaraiMatasa Bismillah: APC ta tsayar da N100m a matsayin kudin takarar shugaban kasa, N50m na gwamna

Jam’iyyar APC tsayar da N100 miliyan a matsayin kudin fom din takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 da ke kara matsowa, LIB ta ruwaito.

An tsayar da kudin ne ne yayin taron gaggawar na kwamitin zartarwar jam’iyyar, NEC wanda tayi a Abuja, yau 20 ga watan Afirilu.

Matasa Bismillah: APC ta tsayar da N100m a matsayin kudin takarar shugaban kasa, N50m na gwamna
Matasa Bismillah: APC ta tsayar da N100m a matsayin kudin takarar shugaban kasa, N50m na gwamna

Jam’iyyar ta sanar da kudin fom din takarar gwamna a N50 miliyan, majalisar dattawa N20 miliyan da majalisar wakilai N10 miliyan.

Inda jam’iyyar ta sanar da fara sayar da fom din takar a ranar Asabar, 23 ga watan Afirilu.

Yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron, sakataran watsa labarai na kasa, Felix Morka, ya ce kudin siyan fom din takarar shugaban kasa zai kama N70 miliyan, yayin da N30 miliyan zai zama na bayyana ra’ayi a Jam’iyyar.

Yayin kwaskwarima ga sanarwar da shugaban matan kungiyar ta kasa, Betta Edu, ta ce za a ba mata fom din kyauta.

Morka ya ce za’a ba wa mata fom kyauta, amma zasu biya kudin bayyana ra’ayinsu kadai.

Babban taron APC: Jerin sunayen ‘yan takarar shugaba Buhari da gwamnoni su ka sauya

Wasu daga cikin ‘yan takarar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke marawa baya sun sha kashi a wajen babban zaɓen jam’iyyar APC na ƙasa. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

An sauya ‘yan takarar shugaba Buhari

A wajen babban taron jam’iyyar wanda ya gudana a dandalin Eagle Square, ranar Asabar, aƙalla huɗu daga cikin ‘yan takarar da ke da goyon bayan shugaba Buhari kafin taron, aka sauya.

Sai dai sanata Abdullahi Adamu, wanda shine na farko a cikin ‘yan takarar da shugaba Buhari ya zaɓa ya samu kujerar shugabancin jam’iyyar.

‘Yan takara 6 ne su ka janye masa kafin a fara babban taron, inda Sanata Musa, ɗaya daga cikin su ya bayyana cewa mataki mai matuƙar wahala.

A wata takarda mai shafi 12 wanda aka raba a farkon taron, gwamnoni 22 na jam’iyyar sun bayyana mutum 78 domin samun kujeru a jam’iyyar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe