24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Filato: Bayan bidiyon wasu ‘yan sanda ya bayyana su na amshe kudaden ‘yan acaba akan titi, hukuma ta yi ram da su

LabaraiFilato: Bayan bidiyon wasu ‘yan sanda ya bayyana su na amshe kudaden ‘yan acaba akan titi, hukuma ta yi ram da su

Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta kama jami’anta 2 da aka dauki bidiyonsu su na amsar rashawa a hannun ‘yan acaba da ke kan titin Kadarko da ke karkashin karamar hukumar Wase da ke jihar ranar 16 ga watan Afirilu.

Kakakin rundunar, ASP Gabriel Ubah ne ya sanar da hakan ta wata takarda wacce ya saki, LIB ta ruwaito.

POLICE OFFICER
Filato: Bayan bidiyon wasu ‘yan sanda ya bayyana su na amshe kudaden ‘yan acaba akan titi, hukuma ta yi ram da su

A cewarsa, cikin wadanda aka kama sun hada da; John Godwin AP/N0302444 INSP da Salihu Garba AP/NO302376/ INSP daga 66 PMF.

Ubah ya bayyana yadda kwamishinan ‘yan sandan, Batholimew Onyeka, tare da tawagarsa ta yaki da rashawa, ya lashi takobin kawo karshen hatsabiban jami’an tsaron da ke yiwa doka karan tsaye a karkashin mulkinsa.

Ya ce sun dauki wannan matakin ne don ya zama darasi ga sauran masu halayya irin tasu.

Ga bidiyon a kasa:

An gwangwaje matukin adaidaita sahu da N3m sakamakon azabtar da shi da ‘yan sanda suka yi

Hukumar ‘yan sanda ta baiwa wani direban Dan sahu mai suna Dayyabu Auwalu diyyar Naira miliyan uku.
Hakan ya biyo bayan umarnin wata babbar kotun tarayya da ke Kano, bayan da wasu ‘yan sanda suka far wa Auwalu a yayin da yake gudanar da harkokinsa.

Jami’an ‘yan sandan da kotun ta samu da laifin sun hada da Abdullahi Daura da tsohon DPO na ofishin ‘yan sandan Kuntau da ke Kano, CSP Abdullahi.

Da yake sanar da hakan a shafin sa na Facebook, lauyan Auwalu, Barista Abba Hikima ya ce, “muna fatan hakan zai zama izina ga sauran jami’an ‘yan sanda da ke cin zarafin jama’a, da kuma ita kanta hukumar.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe