23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Matar aure ta haihu a bandakin asibiti, ba ta taba sanin tana da juna biyu ba

LabaraiMatar aure ta haihu a bandakin asibiti, ba ta taba sanin tana da juna biyu ba

Wata matar aure bata taɓa sanin tana ɗauke da juna biyu ba har sai lokacin da ta ga hannun jaririn ta a cikin robar ɓandaki yayin da take ƙoƙarin ƙwarara ruwa bayan ta gama amfani da shi. Shafin LIB ya ruwaito

Lalene Malik, mai shekaru 23, ‘yan’uwan ta sun garzaya da ita zuwa asibitin A&E a Northwick Park Hospital, cikin Harrow, birnin Landan, bayan tayi ƙorafin tana fama da matsanancin ciwon ciki a gidan ta dake a Greenford, west London, ranar 26 ga watan Maris.

Ta sha magungunan hana ɗaukar juna biyu

Ta bayyana cewa tana shan magungunan hana ɗaukar ciki, sannan kuma tayi gwajin juna biyu har sau biyu a watan Fabrairun 2022 inda su ka nuna bata ɗauke da juna biyu.

Saboda haka kawai sai ta ɗauka cewa ciwon cikin na ta ɓacin ciki ne kawai.

Da ciwon yayi ƙamari an garzaya da ita zuwa asibiti. A lokacin da take jiran a duba ta a asibitin, Lalene ta shiga banɗakin asibitin, inda mahaifiyar ta Sumra, ta jiyo ta tana rafka kuka wanda hakan ya sanya ta sanar da likitocin asibitin.

Lalene ta bayyana cewa:

Na rasa abin cewa, an kai ni wani ɗaki na daban saboda ina ta kuka ni da mahaifiyata.

Abin ban tsoro ne sosai a gare mu sannan naji cewa kamar rayuwata na cikin haɗari

Mahaifiyata ta fara kuka sannan ta ce min ‘baki san kina ɗauke da jariri ba? Daganan na rasa abin cewa.

An samu nasarar ceto rayuwar jaririn

Likitocin da su ka ceto jaririn sun bayyana cewa ‘yayi kama da gawa’ sannan baya numfashi a lokacin amma an samu nasarar ceto rayuwar sa.


Juna biyu
Matar aure ta haihu a banɗakin asibiti, ba ta taɓa sanin tana da juna biyu ba

Jariri Mohammed Ibrahim yana cikin ƙoshin lafiya yanzu bayan likitoci sun bashi kulawar da ta dace. 

Ɗaya daga cikin mata 2,500 masu juna biyu ba su sanin cewa suna da ciki har sai sun haihu.

Ta ɗora laifin akan likitan ta

Lalene ta bayyana cewa ɗan ta wata mu’ujiza ce, amma sai dai ta zargi likitan ta da rashin yin gwaje-gwajen da su ka kamata waɗanda da sun nuna tana ɗauke da ciki.

Da na san cewa ina ɗauke da juna biyu da naji daɗin lokutan wajen zuwa siyayyar kayayyakin jarirai. A cewar ta


Mijin ta yana ƙasar waje a lokacin sannan yayi matuƙar mamaki bayan ya samu labarin haihuwar.

Ɗalibar wacce take karatun digirin ta na biyu a fannin siyasar ƙasa da ƙasa a jami’ar Roehampton, ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta da niyyar haihuwa inda take shan magungunan hana ɗaukar ciki daga watan Oktoba zuwa Janairu wanda likitan ta ya rubuta mata.

Tun bayan mahaifiyar mijina ta fado daki ta tarar muna kwanciyar aure da danta ta daina min magana, Matar aure

Wata mata ta koka akan yadda mahaifiyar mijinta ta dena mata magana bayan ta shiga dakin baccinsu ba tare da kwankwasawa ba, ta tarar da ita da mijinta suna tarayya ta auratayya.

Kamar yadda ta bayyana, lamarin ya auku ne bayan surikarta ta kawo musu ziyara na ‘dan wani lokaci, Pulse ta ruwaito.

Tuko.co.ke ta ruwaito yadda matar ta labarta yadda a duk lokacin da mahaifiyar mijinta na nan take kokarin ganin ta janyo rudani tsakaninta da mijinta.

Yayin bada labari, ta bayyana yadda dattijuwar matar, lokacin da ta kawo musu wata ziyara, ta banka cikin dakin baccinsu, inda ta tarar da ita da mijin suna biyawa juna bukatar aure.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe